Gwamnan APC ya fatattaki jami'an gwamnatinsa 2 a kan kin bin ra'ayinsa

Gwamnan APC ya fatattaki jami'an gwamnatinsa 2 a kan kin bin ra'ayinsa

- Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya fatattaki wasu jami'ai 2 masu kula da kananan hukumoni a kan rashin goyon bayansa

- Sun ki sanya hannu a wata takarda wacce ya nemi duk wani mabiyinsa ya saka hannu a kai don barranta daga Anyim

- Wadanda ya kora sun ce ba za su mara masa baya su ci zarafin Anyim ba, wanda kowa ya san babban mutum ne

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya fatattaki wasu jami'an kula da kananun hukumomi 2. Dama ya fara fatattakar ma'aikata tun bayan ya canja sheka.

Ya kori Okorie Daniel na Ivo DC da Fabian Ivoke na Echiele DC, saboda kin amincewa da wata takarda da suke tunanin za ta bata sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim.

Anyim abokin tafiyar Umahi ne, kafin ya koma jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP, a ranar 20 ga watan Nuwamba, Premium times ta wallafa.

Manyan mutanen Ivo sun taru a Abakaliki ranar Laraba don su mara wa gwamnan baya akan canja shekar da yayi.

Tsofaffin 'yan majalisar tarayya da na jiha, da kuma wadanda har yanzu suke kan mulki, da sauran manyan mutane sun samu damar halartar taron.

KU KARANTA: Taiwo Olowo: Basaraken da aka dade ba a yi mai arziki irinsa ba a Legas, yadda ya tara kudinsa

Gwamnan APC ya fatattaki jami'an gwamnatinsa 2 a kan kin bin ra'ayinsa a wani taro
Gwamnan APC ya fatattaki jami'an gwamnatinsa 2 a kan kin bin ra'ayinsa a wani taro. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: UGC

Sannan shugabannin kananun hukumomi, mataimakansu, shugabannin Ivo, shugabannin gargajiya da na kungiyoyi da sauran manyan masu fada a ji a jam'iyyar APC sun samu halartar taron.

Kamar yadda takardar tazo, wacce kwamishinan labarai, Uchenna Orji ya saki, shugabannin sun bai wa gwamnan goyon baya dari bisa dari a kan canja shekar, sannan sun nisanta kansu daga ayyukan Anyim, dan karamar hukumar Ivo.

"Mu mutanen kirkin karamar hukumar Ivo mun nisanta kawunanmu daga ayyukan dan mu na anguwar Ishiagu, wanda yake kan gaba a harkokin PDP ba tare da amincewar mutanen Ivo ba.

"Yaje can yayi harkokinsa domin mutanen karamar hukumar Ivo basu bayansa.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke mai fyade, masu satar babura da masu garkuwa da mutane a Katsina

"Duk da ya taba rike kujerar shugabancin majalisar dattawa na tsawon shekaru 3, sannan ya rike matsayin sakataren gwamnatin tarayya na shekaru 4, ba tare da ya amfani karamar hukumar Ivo ba, balle yankin kudu maso gabas, sai dai kashe-kashe da tashin hankula," takardar tace.

Wani bangare na takardar ne ya fusata wasu mutane, ciki har da mutane 2 da Umahi ya fatattaka a kan sun ki sanya hannu a kan takardar.

Okorie, daya daga cikinsu ya sanar da manema labarai cewa zai goyi bayan Umahi a komai, amma ba zai yarda a tozarta Anyim ba. Ya ce a yi siyasa kuma a yi adawa, amma ban da zagin manya.

A wani labari na daban, majalisar tarayya ta umarci kwamitin sadarwa da ta gayyaci ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami, don ta fahimtar dashi bukatar samar da mafita a kan tsaro ta ma'aikatarsa.

Kamar yadda takardar ranar Laraba tazo, wacce Ezrel Tabiowo, mai bayar da shawara na musamman ga shugaban majalisar tarayya a kan yada labarai yace, an yanke wannan shawarar ne saboda ganin halin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng