Bidiyon mugun dukan da sojoji suka yi wa budurwa a kan kin gaiashesu ya janyo cece-kuce

Bidiyon mugun dukan da sojoji suka yi wa budurwa a kan kin gaiashesu ya janyo cece-kuce

- Ya dakeni kamar bakuwar karya, cewar wata budurwa a kan wani sojan Najeriya

- A cewarta, tana cikin tafiyarta, ko kallonsu bata yi ba, sai ta ji bulala a gadon bayanta

- Ga mamakinta, sai sojan yace wai ta wucesu bata gaishesu bane shiyasa ya zaneta

Wata budurwa mai suna Olaide Oluwo, tana bukatar a yi mata adalci bayan wani sojan Najeriya da ke Sangotedo, jihar Legas ya ci zarafinta a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda ta wallafa bidiyonta a kafar sada zumuntar zamani, wanda tace ya ci zarafinta ne saboda ba ta gaishesu ba.

"Wannan al'amarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma. Ban yi musu komai ba. Ko kallonsu ban yi ba, sai ga daya daga cikinsu da bulala, ya fara bugu na kamar jaka! Ina cikin tafiya ya zage ni kuma ya bi ni yana duka da bulala.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke mai fyade, masu satar babura da masu garkuwa da mutane a Katsina

Bidiyon mugun dukan da sojoji suka yi wa budurwa a kan kin gaiashesu ya janyo cece-kuce
Bidiyon mugun dukan da sojoji suka yi wa budurwa a kan kin gaiashesu ya janyo cece-kuce. Hoto daga @Olaideoluwo
Asali: Twitter

"Da mutane su ka tambayesa dalilin yin hakan, sai yace na wuce su ba tare da na gaishesu ba, shiyasa ya dauki wannan hukuncin a kaina," a cewarta.

KU KARANTA: Bidiyon soji suna ragargaza 'yan bindiga a dazuzzukan Birnin Kogo daga Ajjah

A wani labari na daban, 'yan uwa da abokan arzikin Theresa Yohanna Bwai, mai shekaru 52 da danta, Bweifar Isaac, mai shekaru 22, suna cikin matsanancin tashin hankali.

Matar ta fadi ta mutu bayan ta samu labarin mutuwar danta daya tal a jihar Filato, shafin Linda Ikeji ya bayyana hakan.

Kamar yadda bayanai suka kammala, wasu 'yan ta'adda sun harbi Isaac, mai shekaru 22, wanda mawaki ne, mai daukar hoto kuma dalibi ne a jihar Jos, ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba da daddare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng