Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan

Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan

- Ben Ayade, gwamnan jihar Cross River ya daura ragamar kula da lafiyar Joseph Wayas a kan gwamnatin jiharsa

- Tsohon shugaban majalisar tarayyan yana wani asibiti a London tun 2013 yana fama da matsanancin ciwo

- Bayan gano hakan ne gwamnan ya umarci kwamishinan lafiyar jiharsa da ya tabbatar yayi iyakar kokarinsa a kai

Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya umarci Betta Edu, Kwamishinan lafiya, da ya kula da lafiyar Joseph Wayas, tsohon shugaban majalisar dattawan, da yake jinya a London, Amurka.

Tsohon shugaban majalisar dattawan yana London yana fama da wani ciwo, wanda har yau ba a fadi cutar ba, tun shekarar 2013, jarida The Cable ta wallafa.

A wata takarda ta ranar Laraba, Christian Ita, Kakakin gwamnan, ya ce gwamnan ya umarci kwamishinan da ya tabbatar ya kula da lafiyar Wayas.

"Bayan samun labarin halin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Joseph Wayas yake, wanda har yanzu yana London yana fama da ciwo. Mai girma gwamna Ben Ayade ya daurawa gwamnatin jihar Cross River ragamar kula da lafiyarsa," kamar yadda Ita yace.

KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar dattawa za ta gayyaci Pantami a kan hauhawar rashin tsaro

Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan
Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Daga yanzu, gwamnan ya umarci kwamishinan lafiyar jihar, Dr Betta Edu, da yayi gaggawar tafiya London don tabbatar da ya kula da lafiyarsa.

"Gwamnan ya umarci kwamishinan da ya tabbatar an biya duk wani kudi da yakamata a biya don tabbatar da Dr. Wayas ya warke."

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke mai fyade, masu satar babura da masu garkuwa da mutane a Katsina

A wani labari na daban, gwamnonin kudu-kudu sun koka a kan rashin cigaban yankinsu, sun ce da dukiyar yankinsu ake bunkasa sauran yankuna, The Cable ta wallafa.

Ifeanyi Okowa, shugaban gwamnonin kudu-kudu, ya fadi hakan a ranar Talata a wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari suka yi.

Abubuwan da suka tattauna a taron yana kun she a cikin wata takarda da Kelvin Ebiri, hadimin gwamnan jihar Rivers na musamman a kan harkar labarai ya fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel