Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya

Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya

- Najeriya ce ƙasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya acewar ƙungiyar ƙididdigar ta'addanci ta duniya (GTI)

- Rahoton GTI ya bayyana cea adadin mutanen da suka mutu sakamakon yakin Boko Haram ya daga shekarar 2018 zuwa 2018

- Kasar Afghanistan ce a mataki na farko, sai kuma kasar Iraq a mataki na biyu, a jerin kasashen da ta'addanci ya shahara

Najeriya ta riƙe kambunta na kasancewa ƙasa ta uku wadda ta'addanci ya yiwa katutu a duniya a cewar ƙungiyar ƙididdigar ta'addanci ta duniya (GTI).

Rahoton da ƙungiyar ta fitar ya nuna cewa adadin yawan mace-mace sanadiyyar ayyukan ƙungiyar Boko Haram ya ƙaru da kaso 25% daga shekarar 2018 zuwa 2019.

Sun kawo misalin harin da aka kaiwa masu jana'izar gawa a garin Badu, Jihar Borno, shekarar 2019, wanda ya kasance mafi muni cikin hare haren ƙungiyar.

KARANTA: Ganduje ya bayar da umarnin sauya wa gidan Zoo matsuguni daga cikin birni

GTI ta gano cewar, sanadiyyar ƙaruwar masu mace-mace daga hare haren ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas ɗin ƙasar, Najeriya itace ƙasa ta biyu da ta samu raguwar adadin mace mace sanadiyyar ta'addanci da hargitsi.

Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya
Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya @Premiumtimes
Asali: Twitter

"Najeriya ta samu gurbi na biyu a ƙasashen da suka samu raguwar mace mace, aƙalla an samu raguwar masu mutuwa da kaso 72% sanadiyyar ayyukan Fulani makiyaya masu tsattsauran ra'ayi", a cewar rahoton.

"Duk da wannan raguwar mace mace, ayyukan ta'addanci Boko Haram ya ƙaru da kaso 25% daga shekarar 2018 zuwa 2019.

"Rahoton ya ce an kashe mutane 2,043 sanadiyyar ayyukan ta'addanci mabambanta a shekarar, amma guda 1,245 kacal aka shigar a rubuce a shekarar 2019."

KARANTA: Nyesom Wike: Buhari zai cinnawa Najeriya wuta idan ya ƙi biyan buƙatun jama'a

A jumullance,mace mace sanadiyyar ta'addanci a duniya ya ragu da kaso 15.5% daga shekarar 2018 zuwa 2019.

"Mace mace daga ta'addanci a Najeriya yanzu haka yai kaso 83%, ƙasa da adadin shekarar 2014 wanda shine mafi yawa da aka samu a tarihin ƙasar.

GTI sun ƙara da cewa har yanzu Najeriya na cikin haɗari sakamakon sabunta ayyukan a ta'addanci da ƙungiyar Boko Haram ta yi a ƙasar da maƙwabtanta irinsu Nijar,Kamaru,da Chadi,wanda ya hakan ya zamewa yankin babbar barazana.

"A shekarar 2019, Boko Haram ta aiwatar da hare-haren ƙunar baƙin wake guda 11 wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 68, hare haren ƙunar baƙin wake suna da kaso 6% cikin mace mace sanadiyyar ayyukan ta'addancin Boko haram a shekarar 2019.

Dukda haka an samu raguwar adadin mace mace sanadiyyar ƙunar baƙin wake da kaso 89% cikin adadin shekarar 2017 wadda aka adadin da ba'a taɓa samun irinsa ba.

"An kashe mutane aƙalla 70, inda 10 suka jikkata a hare haren shekarar 2019. Ɓangarorin biyu na ƙungiyar; wato ISWAP mabiya Albarnawi da Boko Haram mabiya Shekau, dukkaninsu suna yaƙi ne da gwamnatin Najeriya.

GTI tace ta'addancin ɓangarorin biyu ya shafi fararen hula da yawa, musamman a Arewa maso gabas.

Ƙididdiga ta yi nuni da cewa cigaba da kawo hari da ƙungiyoyin ke yi, ya tilastawa sama da mutum miliyan biyu barin muhallansu, inda ƴan Najeriya 240,000 suka yi balaguro zuwa maƙwabtan ƙasashe.

Legit.ng Hausa ta rawaito gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya na shawartar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a kan ya tabbatarwa da ƴan Najeriya cewa a shirye yake ya biya musu buƙatunsu.

Wike ya ce shugaban ƙasar zai jawo ƙasa ta kama da wuta idan har yaƙi biyan buƙatun roƙon da shugabannin al-umma.

Shugabanni sun yi roƙon a biya musu buƙatun al-ummarsu yayin wata tattauna da ƙusoshin fadar shugaban ƙasa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng