Gwamna Okowo ya bukaci ƴan Najeriya su yi karatun ta nutsu, su koma ga Allah
- Dakta Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta, ya bukaci 'yan Najeriya su mika al'amuransu ga Allah
- A cewar gwamnan, alhakin jama'a ne su ririta rayuwarsu saboda al'amura sun rincabe a Nigeria
- Kiran gwamnan na zuwa, a daidai lokacin da wani Malamin addinin Musulunci, Murtadha Gusau, ya yi huduba a kan muhimmancin zaman lafiya
Gwamnan jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa a ranar Juma'a, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi karatun ta nutsu a kan rayuwarsu da al'amuransu, su koma ga Allah sakamakon rikicewar abubuwa a ƙasa.
Gwamnan yayi kiran ne a wurin taron tunawa da mutuwar mataimakin gwamnan farar hula na farko a jihar, Mr Simeon Ebonka, wanda akayi a Makarantar Owa Model Sakandire, Boji-Boji Owa a ƙaramar hukumar Ika North East.
KARANTA: An dawowa da Nigeria gunkin Ife Terracotta mai shekaru 600 daga kasar Netherlands
Ya ce ya zama tilas mutane su ririta rayuwarsu, saboda rincaɓewar lamura a ƙasa.
"Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, mu roƙe shi don kuɓuta daga wannan ƙangin.
Acewarsa, "babu ragowar lokacin da ya rage mana; wannan shine lokacin tunkarar Allah mu gyara dangantakarmu.
Wannan shine lokacin biyayya ga umarnin ubangiji, mu yi aiki mai kyau. Allah ya yi umarnin mu so maƙwabtanmu da makusantanmu kamar yadda zamu so kanmu."
KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya
Okowa ya bayyana cewa kowa yana buƙatar komawa ga Allah don sake ginawa da daidaita alaƙa.
"Yana da muhimmanci mu aikita abin da Allah yace, mu cigaba da bin tafarkinsa don moriyar mu da al-umma baki ɗaya", a cewarsa.
Ya shawarci mutane su cigaba da bin tafarkin ubangiji.
"Hakan zai yi maka amfani idan ka bar duniya, ubangiji zai karɓe ka kuma mutane zasu yi maganar kirki akanka," a cewar Okowa.
A cikin hudubar Malamin addinin Musulunci da Legit.ng Hausa ta wallafa, Murtadha Gusau, ya yi kira tare da yin nuni a kan yadda addinin Musulunci ya bawa zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama'a muhimmanci.
Murtadha ya kawo hujjoji daga cikin Qur'ani da Hadithai daban-daban a cikin hudubar tasa da aka wallafa ranar Juma'a
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng