Matar aure nake buƙata amma bazawara mai hankali, Matashi

Matar aure nake buƙata amma bazawara mai hankali, Matashi

- Wani mutum a jihar Akwa Ibom yana neman matar da zasu angwance a farkon shekara mai kamawa

- Yarima Anitreasure James ya na neman budurwar da zai aura idan kuma uwa ce ya kasance ýaýanta basu wuce 3 ba

- Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce yana bukatar wadda aka taba yaudara a baya

Wani mutum daga Uyo, jihar Akwa Ibom, Yarima Anitreasure James ya na matukar neman matar da zai aura a shekara mai zuwa.

Da ya ke bayani a shafin sa na Facebook ranar Alhamis 36 ga watan Nuwamba, mutumin wanda ya karanci Injiniyanci a jami'ar Uyo, ya fi bukatar wadda aka taba yaudara.

Idan kuma ta taba aure ya kasance yayanta ba su wuce uku ba.

Matar aure nake bukata amma bazawara mai hankali, Matashi
Matar aure nake bukata amma bazawara mai hankali, Matashi. Hoto: Prince Anitreasure James
Source: Facebook

"Maganar gaskiya ina bukatar budurwa daga Akwa Ibom wadda za mu iya aure shekara mai kamawa. Idan kuma uwa ce ya kasance ýaýanta basu wuce 2 zuwa 3 ba amma ya zama cewa an taba yaudarar ta a baya," kamar yadda ya wallafa.

DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Matar aure nake bukata amma bazawara mai hankali, Matashi
Matar aure nake bukata amma bazawara mai hankali, Matashi. Hoto: Prince Anitreasure James
Source: Facebook

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

An dade ba a ga Wayas ba a cikin mutane a shekarun baya bayan nan.

Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross River wanda ya tabbatar da rashin lafiyar tsohon shugaban majalisar ya ce jihar zata dauki nauyin yi wa dattijon kasar magani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel