Korona ta yi ajalin tsohon Farai Ministan Sudan

Korona ta yi ajalin tsohon Farai Ministan Sudan

- Tsohon firayi ministan Sudan Al-Mahdi ya rasu lokacin da ya ke jinya a wani asibiti a kasar Dubai

- Ya kwanta a asibiti tsawon kwanaki sakamakon matsanancin sarkewar numfashi da annobar Coronavirus ya haddasa

-Za a yi jana'izarsa a birnin Khartoum a garin Omdurmanfu kuma za a binne shi a makabartar kakansa Mohammad Ahmed Al-Mahdi

Tsohon firai ministan kasar Sudan Sadiq Al-Mahdi kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Umma ya rasu ya na da shekara 84 bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Firai ministan kasar na karshe ya rasu jiya, sati uku bayan kwantar da shi a wani asibiti da ke Dubai.

Korona ta yi ajalin tsohon Farai Ministan Sudan
Korona ta yi ajalin tsohon Farai Ministan Sudan. Hoto: Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Kamar yadda kafafen labaran kasar Sudan su ka ruwaito, jikin Al-Mahdi ya tsananta bayan fama da mummunar sarkewar numfashi da cutar ke haddasawa.

An kifar da gwamnatin Al-Mahdi ne lokacin juyin mulkin da shugaba Omar Al-Bashir yayi ya zama shugaban kasa. Jam'iyyarsa ta hade kai da babbar jam'iyyar Sudan kuma su ka yi sanadiyar da sojoji suka hambarar da Al-Bashir a watan Afrilun da ya gabata.

KU KARANTA: Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira miliyan 500 daga wurin kakakin majalisa

Ya na daya daga cikin wanda ba sa goyon bayan wutar ricikin da ke faruwa tsakanin Sudan da Isra'ila, saboda wariyar launin fatan da ta nunawa Palestiniwa.

Gwamnatin rikon kwarya da sojoji suka kafa ta bada kwana uku saboda nuna alhini.

A wata sanarwa da jam'iyyar sa ta fitar, za a kawo gawar Al-Mahdi birnin Khartoum gobe da safe kuma an shirya jana'izarsa a garin sa na Omdurmanfv, da ke jihar Khartoum, kuma an shirya binne sa a makabartar kakansa Mohammad Ahmed Al-Mahdi

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164