'Yan sandan Zamfara sun ki karbar toshiyar baki ta N250,000, sun kama ɓarawon mota

'Yan sandan Zamfara sun ki karbar toshiyar baki ta N250,000, sun kama ɓarawon mota

- 'Yan sanda sun kama wani da suka yi zargin ɓarawon mota ne bayan ya yi yunkurin basu cin hancin ₦250,000

- Mutumin dan asalin Gidan Dare da ke Jihar Sokoto ya yi yunkurin ba wa yan sanda cin hanci bayan ya gaza ba su gamsassun bayanai kan motar da ya ke ciki

- Da ake bincike, ya ce wani dan uwan harkallarsa Abdullahi ne ya sato motar ranar 15 ga Nuwamba 2020

'Yan sandan jihar Zamfara sun kama wani da ake zargin hatsabibin ɓarawon mota ne bayan sun ki karbar cin hancin naira 250,000 daga wajensa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar, SP Shehu Muhammad, shi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau ranar Talata.

'Yan sandan Zamfara sun ki karbar cin hancin N250,000, sun kama ɓarawon mota
'Yan sandan Zamfara sun ki karbar cin hancin N250,000, sun kama ɓarawon mota. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Muhammad ya bayyana cewa wasu jami'an yan sanda da ke aiki kauyen Tazame kan titin Gusau zuwa Zaria sun kama wani mutum da ake kyautata zaton ɓarawon mota ne, Surajo Ibrahim wanda ya fito daga Gidan Dare a Jihar Sokoto.

Ya ce an kama wanda ake zargin cikin wata mota kirar Toyota Matrix kuma lambar motar ABC 585 AP.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka 'yan bindiga 82 a Katsina da Zamfara, Hedkwatar Tsaro

"Wanda ake zargin ya kasa gabatar da bayanai masu amfani ga jami'an da suke aiki kuma yayi kokarin biyan su naira 250,000 don kada su kama shi, wanda hakan yasa yan sandan suka tsananta zargi a kansa," a cewar Muhammad.

Lokacin bincike, wani dan uwan harkallar sa, mai suna Abdullahi, da ke zaune a Abuja, shi ne ya sato motar ranar 15 ga Nuwambar 2020.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel