Da duminsa: Majalisar dattawa za ta gayyaci Pantami a kan hauhawar rashin tsaro

Da duminsa: Majalisar dattawa za ta gayyaci Pantami a kan hauhawar rashin tsaro

- Kwamitin sadarwa na majalisa dattawan Najeriya ta jaddada bukatar kiran gaggawa ga Dr. Isah Ali Pantami

- Kamar yadda shugaban kwamitin ya sanar da manema labarai, ya ce hakan ya zama dole ganin yawaitar rashin tsaro a kasar nan

- Shugaban kwamitin ya ce miyagu na amfani da kafafen sadarwar zamani wurin karbar fansa bayan sun sace mutane

Majalisar tarayya ta umarci kwamitin sadarwa da ta gayyaci ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami, don ta fahimtar dashi bukatar samar da mafita a kan tsaro ta ma'aikatarsa.

Kamar yadda takardar ranar Laraba tazo, wacce Ezrel Tabiowo, mai bayar da shawara na musamman ga shugaban majalisar tarayya a kan yada labarai yace, an yanke wannan shawarar ne saboda ganin halin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.

A cewar sanatan, matsaloli irin na garkuwa da mutane, fashi da makamai, kisan kai da sauran ta'addancin da Najeriya take fuskanta sun yi yawa, Daily Trust ta tabbatar.

KU KARANTA: Gagarumin mai arziki ya bai wa ma'aikacinsa kyautar Euro miliyan 21

Da duminsa: Majalisar dattawa za ta gayyaci Pantami a kan hauhawar rashin tsaro
Da duminsa: Majalisar dattawa za ta gayyaci Pantami a kan hauhawar rashin tsaro. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Kisan shugaban APC na jihar Nasarawa da sauran kashe-kashen mutane da aka yi a kasar nan yana nan a cikin zuciyarmu."

Ya kara bayyana damuwarsa a kan yadda yakamata a ce wadanda suke kula da rayukan jama'a suka fara taimakon 'yan ta'adda.

Abu mafi tsoratarwa shine yadda ake ta kama jami'an tsaro da dama masu hannu dumu-dumu a kan fashi da makami da garkuwa da mutane a cikin kasar nan. A Najeriya ne kadai ba a yin amfani da harkar sadarwa wurin gano mutane.

Ya daga maganar yadda 'yan ta'adda suke amfani da waya wurin tattaunawa da iyaye da 'yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su, kuma su amsa kudi ba tare da an kamasu ba, ta yaya za a yi a ce ba a amfani da irin wannan damar wurin damkarsu?

Majalisar tarayya ta koka a kan yadda matasa suka yi ta yadda suka ga dama da sunan zanga-zangar EndSARS.

KU KARANTA: An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga a Katsina, an ceto wata mata

A wani labari na daban, an hana sanatoci damar ganin Ndume a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja. An garkame shi a ranar Litinin saboda rashin samun damar bayyana tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, wanda ya tsaya wa.

Alkali Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umarci a damke Ndume bayan wanda ya tsaya wa ya kasa bayyana a kotu a kan zargin satar naira biliyan 2 na kudin fansho, Daily Trust ta ce.

Masu rajin kare hakkin bil'adama suna bukatar a saki Ndume iya wuya. Duk da bayanai sun kammala a kan yadda aka ga sanatoci suna kai-kawo a gidan gyaran hali don ganin Ndume a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel