Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci

Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci

- Gwamnn Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da uwargidansa, Hafsat Ganduje sun dade da yin aure

- Wasu tsoffin hotunansu yayin da suke shan amarci sun bayyana wadanda suka ja hankulan jama'a

- A hoton, an gan su rike da kwalbar lemu kuma sanye da kayan hausawa a wata liyafa da aka yi kasar nan

Gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da matarsa mai suna Hafsat Umar Ganduje sun dade da aure.

Sun yi shekaru aru-aru tare inda suka hayayyafa kuma hatta ''ya'yansu suka hayayyafa, hakan ne yasa suke da jikoki.

Wani hoton tuna baya na ma'auratan ya bayyana a yayin da suke ganiyar cin amarcinsu bayan aurensu.

Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci
Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

An ga ma'auratan tsaye rike da kwalaben lemu a yayin da suka halarci wata liyafa a cikin kasar Najeriya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Gwamonin Kudu: Ma'adanan yankinmu ake amfani da su amma an bar mu cikin mawuyacin hali

Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci
Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

A hoton wanda bashi da kala, an gansu sanye da kayan gargajiya na al'adar malam bahaushe.

Ganduje yana sanye da babbar riga tare da hula, yayin da uwargidansa ke sanye da zani da riga rike da dan mayafinta a hannu.

A hoton, a bayyana yake tsananin kuruciyar ma'auratan.

KU KARANTA: Hukumar kurkukun Kuje ta saka takunkumi, ta hana 'yan majalisa ganin Ndume

A wani labari na daban, a kalla 'yan bindiga 67 dauke da miyagun makamai suka sheka lahira yayin da wasu suka samu rauni sakamakon ragargazar da dakarun sojin saman rundunar Operation Hadarin Daji a dajin Birnin Kogo a Katsina.

Duk a lokaci daya, an samu kashe wasu 'yan bindiga 15 a dajin Ajjah da ke jihar Zamfara sakamakon harin sojin saman.

An kai dukkan samamen ne a ranar 23 ga watan Nuwamban 2020 bayan bayanan sirrin da dakarun sojin suka samu.

Jiragen yakin sojin saman dauke da bindigogi sun kai wa dazuzzukan biyu hari inda suka dinga samun nasarar harbin kogunan wadanda suka kasance garkuwa ga 'yan bindigan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel