Bidiyon soji suna ragargaza 'yan bindiga a dazuzzukan Birnin Kogo daga Ajjah

Bidiyon soji suna ragargaza 'yan bindiga a dazuzzukan Birnin Kogo daga Ajjah

- 'Yan bindiga 67 a kalla masu dauke da makamai dakarun sojin saman Najeriya suka ragargaza a dajin Birnin Kogo

- Wasu 15 sun sheka lahira sakamakon harin da dakarun sojin saman suka kai dajin Ajjah da ke jihar Zamfara

- Hukumar sojin Najeriya ta jinjinawa dakarun tare da sauran jami'an tsaro a kan kokarin kawo karshen ta'addanci

A kalla 'yan bindiga 67 dauke da miyagun makamai suka sheka lahira yayin da wasu suka samu rauni sakamakon ragargazar da dakarun sojin saman rundunar Operation Hadarin Daji a dajin Birnin Kogo a Katsina.

Duk a lokaci daya, an samu kashe wasu 'yan bindiga 15 a dajin Ajjah da ke jihar Zamfara sakamakon harin sojin saman.

An kai dukkan samamen ne a ranar 23 ga watan Nuwamban 2020 bayan bayanan sirrin da dakarun sojin suka samu.

Jiragen yakin sojin saman dauke da bindigogi sun kai wa dazuzzukan biyu hari inda suka dinga samun nasarar harbin kogunan wadanda suka kasance garkuwa ga 'yan bindigan.

Kamar yadda Manjo Janar John Enenche ya fitar a wata takarda, ya ce hukumar sojin Najeriya tana jinjinawa dakarun tare da sauran jami'an tsaron da ke yankin arewa maso yamma.

Ta jinjinawa kwarewarsu tare da kira garesu da su cigaba da ayyukan da suke na ganin karshen 'yan bindigar.

KU KARANTA: Gagarumin mai arziki ya bai wa ma'aikacinsa kyautar Euro miliyan 21

Bidiyon soji suna ragargaza 'yan bindiga a dazuzzukan Birnin Kogo daga Ajjah
Bidiyon soji suna ragargaza 'yan bindiga a dazuzzukan Birnin Kogo daga Ajjah. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa

A wani labari na daban, a ranar Litinin 'yan sandan jihar Katsina suka yi musayar wuta da 'yan bindiga a karamar hukumar Safana yayin kokarin ceto wata mata mai shekaru 55, Hafsatu Idris.

An samu labarin yadda 'yan bindiga suka kai hari kauyen Gamma wuraren karfe 1, lokacin da suka saci Hafsatu, jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce, "Rundunar Operation Puff Adder sun yi musayar wuta a tsaunin Habul da ke dajin Rugu wuraren karfe 4:20 na asuba, inda suka yi bata-kashi da masu garkuwa da mutanen har suka ceci matar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel