Mahaifiya ta rasu washegarin rasuwar dan ta daya tilo a duniya

Mahaifiya ta rasu washegarin rasuwar dan ta daya tilo a duniya

- Wani al'amari mai ban tsoro da al'ajabi ya faru a jihar Filato

- Wata dattijuwar mata ta samu labarin kisan dan ta daya tal

- Take a nan ta fadi, washegari da safe tace ga garin ku

'Yan uwa da abokan arzikin Theresa Yohanna Bwai, mai shekaru 52 da danta, Bweifar Isaac, mai shekaru 22, suna cikin matsanancin tashin hankali.

Matar ta fadi ta mutu bayan ta samu labarin mutuwar danta daya tal a jihar Filato, shafin Linda Ikeji ya bayyana hakan.

Kamar yadda bayanai suka kammala, wasu 'yan ta'adda sun harbi Isaac, mai shekaru 22, wanda mawaki ne, mai daukar hoto kuma dalibi ne a jihar Jos, ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba da daddare.

KU KARANTA: Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa

Mahaifiya ta rasu washegarin rasuwar dan ta daya tilo a duniya
Mahaifiya ta rasu washegarin rasuwar dan ta daya tilo a duniya. Hoto daga Sule Mato.
Asali: Facebook

Bayan ta samu labarin mutuwar danta, Bwai ta yanke jiki ta fadi, ta rasa ran ta washegari da safe.

Za a yi jana'izar uwar da danta a kauyensu Daffo, karamar hukumar Bokkos da ke jihar Filato.

'Yan uwa da abokan arzikin mamacin sun yi ta wallafa rasuwar a shafukansu na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

KU KARANTA: 2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki

A wani labari na daban, a ranar Litinin, wani dan ta'adda ya kai wa wani Malam Nuhu mazaunin kauyen Tumfafi da ke karamar hukumar Garko da ke jihar Kano, hari, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda masu gani da ido suka ce, dan ta'addan yayi yunkurin kashe Nuhu a gidansa kwanakin baya, har yana sharba masa wuka a hannu.

An ce mutumin ya tsere ne bayan ya kashe Malam Nuhu, bayan ganin hakan ne yasa dan Nuhu ya bi mutumin waje da gudu don ya kama shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel