Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata tare da dan na hannun daman Atiku Abubakar

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata tare da dan na hannun daman Atiku Abubakar

- Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari gidan wani dan sanda makusancin Atiku Abubakar

- Kamar yadda makwabta suka tabbatar, sun kai harin ne bayan zargin cewa dan sanda ya iso garin Yolan daga Abuja

- Rashin samunsa ne yasa suka tasa keyar matarsa da dan sa a yankin Yolde Pete da ke karamar hukumar Yola

Wasu miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari yankin Yolde pete da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Mazauna yankin tare da jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, miyagun dauke da makamai sun tsinkayi gidan dansanda makusancin Atiku Abubakar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, an gano cewa 'yan bindigan sun so tarar da dan sandan ne bayan sun zargi sun iso gari tare da Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Hisbah ta kama dan sandan da ke sace yaran mutane domin lalata da su a Kano

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata tare da dan na hannun daman Atiku Abubakar
Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata tare da dan na hannun daman Atiku Abubakar. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

"Miyagun sun yi tsammanin jami'in dan sanda ya iso garin da kudi, don haka suka nemi damkarsa. Rashin samun kama shi ne yasa suka iza keyar matarsa da dan sa daya," mazauna yankin suka ce.

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar, miyagun sun kwashe a kalla minti 30 suna cin karensu babu babbaka, duk da kuwa gidan yana da kusanci da gidan gyaran hali na jihar Adamawan da ke Yola.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ragargaza wasu

A wani labari na daban, Hajiya Bisola Rahama Zakariyya, shugabar Ekkanemi College of Islamic Theology da ke Maiduguri, ta rasu tana tsaka da gabatar da jawabi. Al'amarin ya faru ne a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.

Matar tana sanye da hijabi da takunkumin fuska, tana tsaka da gabatar da jawabi sai ta rasa inda kanta yake, take a nan baki masu saurin tunani suka yi gaggawar zuwa gareta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel