Hotunan tubabbun barayin kayan tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato

Hotunan tubabbun barayin kayan tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato

- Wasu daga cikin wadanda suka saci kayan tallafi a jihar Filato sun tafi har gidan gwamnatin jihar don neman gafara

- Matasan sun dauki wasu daga cikin kayan tallafin da suka rage a hannunsu sun mayar dasu bayan jin wa'azi mai ratsa jiki

- Rev. Dachoma, faston wata babbar coci da ke jihar ne ya jagorance su, bayan ya sanar dasu cewa Ubangiji zai iya fushi dasu

Wasu daga cikin wadanda suka saci kayan tallafi, suka kuma wulakanta dukiyar gwamnati da ta al'umma da sunan neman kayan tallafi suna neman gafarar gwamnatin jihar Filato.

Masu neman gafarar, sun gurfana gaban gwamnatin da kayan da suka sata, suna neman yafiya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Faston wata babbar coci, mai suna Rev. Ezekiel Dachomo, shine ya raka tubabbun har sabon gidan gwamnati da ke Rayfield a Jos, inda ya bayyana yadda suka fadi laifukansu a wani taron addu'a da wata makarantar sakandare ta Zang, wacce take Bukuru a karamar hukumar Jos ta kudu ta shirya.

Faston ya ce fiye da mutane 2000 ne suka gabatar da kawunansu yayin da yake wa'azi a kan sace-sace da illar lalata kayan al'umma na gwamnati.

Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato
Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato. Hoto daga @Lindaikeji blog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci

Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato
Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

A cewarsa, ayyukan bata-garin za su iya janyo fushin Ubangiji garesu da jihar gabadaya. Ya ce zanga-zangar EndSARS tana daya daga cikin ayyukan shaidan da za su iya janyo fushin Ubangiji ga jihar.

Wa'azin da yayi ya taba zukatan wasu daga ciki, har suka yanke shawarar mayar da kayan da suka sata, wadanda har a lokacin suna hannunsu, don neman gafarar wadanda suka satar wa da kuma gudun fushin Ubangiji ya tabbata a garesu.

Rev. Dachomo ya roki gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, da ya gafarta musu don su samu rangwame daga Ubangiji, musamman yadda suka taso da kansu cikin nadama suka taho da kayan har inda yake, sannan sun lashi takobin ba za su sake aiwatar da makamancin haka ba.

Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato
Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur

Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato
Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Abok Atu, wanda ya amshi kayan tallafin a maimakon gwamnan, ya yaba da tsoron Allan wadanda suka gabatar da kawunansu.

A cewarsa, ayyukan bata-garin da suka yi sata sun janyo matsala ga jihar, ba abincin tallafin kadai ba, har da injina, kayan gwamnati da kayan 'yan kasuwa da suke da kimar biliyoyi da aka sace kuma aka lalata.

Farfesa Atu, ya shawarci matasan jihar Filato da su kiyaye yin abubuwan da za su kawo tashin hankali a jihar, sannan ya ce zai sanar da gwamnan don ya yafe musu laifukan da suka aikata.

Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato
Hotunan tubabbun barayin kayana tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

A wani labari na daban, Wata 'yar Najeriya, mai suna Igwe Munachimso, ta ce ya kamata 'yan yankin kudu maso gabas su rage sadakinsu, tun bayan dan uwanta ya auri wata 'yar Benue da sadaki kasa da N50,000.

Munachimso ta bayyana wannan shawararta a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta bayyana abubuwan da aka bukaci yayanta ya kai na al'adar Benue.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel