Yanzu Yanzu: Za a fara sauraron bukatar bayar da belin Ndume a ranar Alhamis
- Za a fara sauraron bukatar neman belin Sanata Ali Ndume mai wakiltan yankin Borno ta Kudu
- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta saka ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba domin fara zama
- An dai tsare Ndume ne bayan ya gaza gabatar da tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina wanda ya tsayawa a matsayin jingina
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, za ta saurari bukatar neman bayar da belin sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume.
An tsare Ndume a gidan yari tun ranar Litinin, kan tsayawa tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, da yayi, inda shi kuma ya tsere.
Maina na fuskantar tuhume-tuhume na zambar kudade har naira biliyan biyu kafin aka bayar da belinsa.
A ranar 18 ga watan Nuwamban 2020, Justis Okon Abang, ya soke belin da aka baiwa Maina, yayi umurnin kama shi sannan ya bayar da izinin ci gaba da shari’arsa a bayan idonsa.
KU KARANTA KUMA: Mutumin da matarsa ta haifi yan uku ya koka, ya roki yan Najeriya su kawo masa tallafi
Alkalin a ranar Litinin, ya kuma tsare Ndume a gidan yari har sai ya gabatar da Maina ko kuma ya biya kudi naira miliyan 500 don belinsa a asusun tarayya.
Alkalin, a yayin ci gaba da zama a bayan idon Maina, a ranar Laraba, ya sa hannu a takardar neman beli da lauyan Ndume ya cike, jaridar The Nation ta ruwaito.
Ya ce an janyo hankalinsa ga bukatar neman belin da misalin karfe 8:58am na ranar Laraba, inda ya bayyana cewa a nan take ya yi umurnin fara sauraron lamarin a ranar Alhamis.
Ya kuma bayyana cewa ya yi umurnin mika takardar lokacin sauraron karar ga bangarorin da abun ya shafa.
KU KARANTA KUMA: Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria
Koda dai lauyan Ndume baya a kotu, lauyan EFFF, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da cewa ya samu takardar fara sauraron lamarin.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Aliyu ya ce sake bayyanar Maina zai dakatar da tozarcin da Ndume ke fuskanta a idon duniya kafin lamarin ya tabarbare.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng