Gagarumin mai arziki ya bai wa ma'aikacinsa kyautar Euro miliyan 21

Gagarumin mai arziki ya bai wa ma'aikacinsa kyautar Euro miliyan 21

- Sakataren wani babban dan kasuwa da ke Ingila ya yi murabus bayan wanda yake yi wa aiki ya ba shi kyautar euro miliyan 21

- Babban dan kasuwar, Mathew Moulding, mai kamfanin Hut Group yana da dukiya mai tarin yawa cikin shekaru 16

- Dan kasuwar ya bayar da kyautar euro miliyan 830 ga ma'aikatansa, wanda hakan ya zama sanadiyyar arzikinsu

Sakataren wani babban dan kasuwan Ingila, Matthew Moulding, ya yi murabus bayan wanda yake yi wa aiki ya bashi euro miliyan 21.

Moulding, mai kamfanin Hut Group ya bayar da kyautar euro miliyan 830 ga ma'aikatansa, shafin Linda Ikeji ya bayyana.

Mutumin mai shekaru 48, wanda ya kaddamar da kamfaninsa da John Gallemore a 2004, ya tara dukiya mai tarin yawa cikin shekaru 16.

Moulding ya fara da sayar da CD ta yanar gizo, amma yanzu yana da shafukan yanar gizo fiye da 100, na siyar da kayan amfanin asibiti da na kwalliya.

KU KARANTA: Maina: Ndume ya kwana a gidan kurkuku, ya bayyana matakin da zai dauka

Gagarumin mai arziki ya bai wa ma'aikacinsa kyautar Euro miliyan 21
Gagarumin mai arziki ya bai wa ma'aikacinsa kyautar Euro miliyan 21. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Kamfaninsa yana sayar da kaya, kayan kwalliya, sannan har wurin sayar da Honda da Nestle ba a bar shi a baya ba.

Ya kaddamar da kamfaninsa mai suna Hut Group na harkar kasuwanci a watan Satumba, ya bayar da euro miliyan 830.

Kamar yadda mutumin mai yara 4 yace, shi mutum ne mai dagewa da kokarin yin aiki tukuru.

KU KARANTA: 2023: DG na PGF a karkashin APC ya bayyana yankin da jam'iyyar za ta mika tikitin ta

Moulding ya yi alkawarin biyan euro 750,000 a matsayin albashi ga gidauniyarsa a matsayin sadaka. Ya kuma bayar da euro miliyan 10 a matsayin tallafin COVID-19, sannan ya bai wa ma'aikatansa kyautar euro miliyan 2 a kan albashinsu.

Ya kuma raba wa wasu ma'aikatansa euro miliyan 1, wanda hakan yayi sanadiyyar azurtasu. Sakatariyar Moulding tana da dumbin dukiya wacce za ta iya bai wa wasu kyauta, duk da har yanzu bata wuce shekaru 36 da haihuwa ba.

Moulding mutum ne mai alheri, don yana bayar da kyautuka ga duk wanda ya kusance shi.

A wani labari na daban, hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta kama wata yarinya 'yar shekara 19, mai suna Jemila Ibrahim da kawarta, Fatima Mohammed, mai shekaru 21 dake Monkey Village wurin Festac Area a Legas.

Ana zarginta da banka wa gidan wani Mohammed Yusuf na Monkey Village a Legas, wacce budurwarsa Rabi, take zaune a gidan, a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng