An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga a Katsina, an ceto wata mata

An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga a Katsina, an ceto wata mata

- Wasu 'yan sandan jihar Katsina sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga a dajin Rugu

- Sun samu nasarar ceto wata mata mai shekaru 55, sannan sun harbi wasu 'yan bindigan

- Da 'yan sandan suka shiga daji bincike, sun ga wasu babura guda 2 marasa lamba

A ranar Litinin 'yan sandan jihar Katsina suka yi musayar wuta da 'yan bindiga a karamar hukumar Safana yayin kokarin ceto wata mata mai shekaru 55, Hafsatu Idris.

An samu labarin yadda 'yan bindiga suka kai hari kauyen Gamma wuraren karfe 1, lokacin da suka saci Hafsatu, jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce, "Rundunar Operation Puff Adder sun yi musayar wuta a tsaunin Habul da ke dajin Rugu wuraren karfe 4:20 na asuba, inda suka yi bata-kashi da masu garkuwa da mutanen har suka ceci matar."

A cewar Gambo, "Rundunar ta samu damar ceto wacce aka yi garkuwa da ita, da kuma wasu babura 2, kirar Bajaj marasa lamba.

"Da yawan 'yan ta'addan sun tsere cikin dajin da raunuka, don sun ga jini sosai a dajin.

"Yanzu haka 'yan sandan suna zagaya dajin ko za su tsinci gawawwaki ko kuma 'yan ta'adda masu rauni, don a samu damar yin bincike."

KU KARANTA: Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas

An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga a Katsina, an ceto wasu mata
An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga a Katsina, an ceto wasu mata. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Makiyaya sun sake kutsawa gidan gonar Falae, sun fatattaki ma'aikata

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne jami'an tsaro su yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da sun dakatar da kashe-kashen da ya ta'azzara a Najeriya.

Shugaban kasan ya fadi hakan ne bayan samun labarin kisan Philip Shekwo, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, jaridar The Cable ta wallafa.

Sai da aka sace Shekwo a gidansa da ke Lafia, ranar Asabar da daddare, daga baya aka tsinci gawarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: