Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci

Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci

- Wani Olumuyiwa, mai yara biyu ya sanar da wata kotu dalilinsa na rabuwa na shekaru 24 da matarsa

- A cewarsa, ya gano matarsa tana lalata da faston cocinsu da kuma wani dattijo wanda yake shiryasu idan sun yi fada

- Bayan ya gano hakan, sai ta dauki wuka za ta sharba masa a ciki don ya mutu ta huta kuma asirinta ya rufu

Wani mutum mai suna Olumuyiwa Johnson, mai yara 2, ya tabbatar wa da wata kotu da take Ibadan cewa ba zai iya zama da matarsa ba.

A cewarsa, aurensa mai shekaru 24 ya kare da matarsa saboda rashin kamun kanta da barazana ga rayuwarsa.

Olumuyiwa, wanda mazaunin wuraren Eleta ne a Ibadan, ya tabbatar wa da alkali Ademola Odunade, cewa matarsa tana barazana ga rayuwarsa bayan ya gano tana lalata da wasu kusoshin cocinsu, Vanguard ta wallafa.

A cewarsa, "Shekaru 24 kenan muna tare da Omotayo, ban taba tunanin za ta iya wannan shaidancin ba. Yanzu haka tana tarayya da faston cocinmu da wani babba duk a lokaci daya.

Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci
Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

"Abinda yake bani mamaki shine yadda kullum take shawarta ta da in dinga zuwa neman tabaraki a wurinsu.

KU KARANTA: Sabuwar cuta ta barke a Filato sakamakon cin wawason tallafin korona

"Ta kai ga ko fada muka yi da ita, su suke sasanta mu. Duk da mutane sun dade suna fadi min, amma bana yarda, har ja musu kunne nake yi a kan su daina shiga harkokin aurenmu. Har daina zuwa cocin nayi, bayan na gano abinda take yi.

"Watarana da daddare, Omotayo ta dauko wuka ta nufeni, zat a sharba min a ciki. Idan na bata kudin makarantar yara, sai ta dinga kashewa tana bushasharta."

Omotayo bata musanta duk laifukan da mijinta ya lissafa ba.

KU KARANTA: A taimaka a rage dukiyar aure ko 'yan mata za su samu shiga, budurwa ta roki iyaye

Don haka alkalin kotun ya amince da rabuwar auren don a samu zaman lafiya. Ya kuma bar wa mijin damar rike yaran a hannunsa.

A wani labari na daban, daya daga cikin iyayen daliban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jihar Kaduna da masu garkuwa da mutane suka sace a makon da ya gabata, ya ce wadanda suka yi garkuwa da diyarsa sun ce za su yi ta lalata da ita matsawar bai yi gaggawar kai kudaden da suka bukata a wurinsa ba.

Daliban, 'yan fannin yaren faransa ne, wadanda suka kama hanyar zuwa NFLV da ke Badagry ne lokacin da aka yi garkuwa da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel