Kakakin majalisar wakilai ya tona asirin dan sandan da ya bindige mai jarida a Abuja

Kakakin majalisar wakilai ya tona asirin dan sandan da ya bindige mai jarida a Abuja

- Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya bayyana sunan jami'in tsaron da ya bindige wani magidanci a Abuja

- Gbajabiamila ya yi alkawarin ganin an tabbatar da adalci kan lamarin

- Ya bayyana alhininsa ga iyalan mamacin kuma yayi alkawarin taimaka musu

Kakakin majaisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana sunan dogarinsa da ya bindige wani mai sayar da jarida a Abuja, Ifeanyi Okereke, ranar Alhamis ba gaira ba dalili.

Gabjabiamila ya ce sunan jami'in tsaron Abdullahi Hassan, kuma tuni ya mika shi hannun hukumar DSS domin hukunta shi.

A jawabin da ya saki ranar Juma'a, Kaakin ya ce ya cire jami'in daga cikin masu tsaronsa yanzu.

"Da safen nan na mika jami'in tsaro, Abdullahi M. Hassan, hannun hukumar DSS domin bincike da hukuncin da ya dace," yace.

"A yanzu dai na dakatad da shi daga tawagar dogarai na."

Kakakin majalisar wakilai ya tona asirin dan sandan da ya bindige mai jarida a Abuja
Kakakin majalisar wakilai ya tona asirin dan sandan da ya bindige mai jarida a Abuja
Asali: Twitter

KU DUBA: Dogarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige mai jarida ba gaira, ba dalili

Kakakin ya jaddada cewa babu wani dalilin da zai sa a hallaka rayuwan mutum haka kawai.

"Mutuwar Mr Ifeanyi Okereke a hannun daya daga cikin jami'an tsaro na ya matukar girgiza ni. Mr Okereke dan kasa ne wanda ke neman abincinsa da na iyalansa," yace

"Sai na tabbatar da cewa iyalan Okereke sun samu adalci."

"Na aika sakon ta'aziyya na ga iyalansa kuma na shirya haduwa da iyayensa."

"Bayan haka, na yi alkawarin taimakawa matarsa da yaran da ya bari."

KU KARANTA: Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a wata jihar Arewacin Najeriya, Shugaban NNPC Mele Kyari

Mun kawo muku rahoton cewa wani jami'in dan sanda dake gadin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige wani mai sayar da jarida a birnin tarayya, Abuja ranar Alhamis.

Kakakin majalisar da kansa ya tabbatar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng