Kotu ta daure yaya da ƙanwa saboda satar naira miliyan 1.7 a Kaduna

Kotu ta daure yaya da ƙanwa saboda satar naira miliyan 1.7 a Kaduna

- Kotu da ke zamanta a Kaduna ta yanke wa yaya da kanwa hukuncin shekaru 10 a gidan gyaran hali saboda satar N1.7m

- An yi karar 'yan uwan biyu ne saboda karkatar da naira miliyan 1.7 da suka karba ta hannun gidauniyarsu a matsayin tallafi ga wani mara lafiya

- Sai dai daga bisani sun ki bawa mara lafiyar kudaden suka kuma karkatar da kudin suka yi amfanin kansu da shi

Wata babban kotu a Jihar Kaduna, a ranar Talata, ta yankewa wasu mata biyu yaya da ƙanwa (Maryam da Rukaiya) hukuncin gidan yari an shekaru 10 saboda satar naira miliyan 1.7 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An gano cewar ƴan uwan biyun da suka mallaki gidauniyar Jamal Health Foundation sunyi amfani da shafinsu na dandalin sada zumunta don neman tallafin kuɗi na taimakawa mara lafiya a 2019.

Kotu ta daure yaya da kanwa saboda satar naira miliyan 1.7 a Kaduna
Kotu ta daure yaya da kanwa saboda satar naira miliyan 1.7 a Kaduna. Hoto @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ƴan uwan sun karkatar da kuɗaɗen da suka samu daga hannun ƴan Najeriya sunyi hidimomin gabansu.

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, cikin sanarwar da Shugaban Sashin Hulda da Jama'ar ta, Wilson Uwujaren, ya fitar ya ce ɗaya daga cikin wanda suka bada tallafi, Badamasi Shanon ya yi ƙorafi kan matan biyu cewa ba suyi amfani da kuɗin don dalilin da suka karba ba.

Wani sashi na cikin sanarwar ta ce, "Wani Alhaji Badamasi Shanono a ƙorafin da ya shigar a 2019 ya yi zargin cewa Gidauniyar Jamal Health Foundation mallakar ƴan uwan biyu ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta ta nemi tallafin kuɗi don yi wa wani Usman Umar magani sakamakon rashin lafiya da ke fama da ita na tsawon shekaru biyu.

KU KARANTA: Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira miliyan 500 daga wurin kakakin majalisa

"Shanono ya yi ikirarin cewa ya bawa gidauniyar tallafin naira miliyan ɗaya yayinda wata mata ta bada N700,000. Ya ƙara da cewa Jamal Health Foundation ta ƙi bawa mara lafiyar kuɗin sai dai ta yi amfani da kuɗaɗen don wasu buƙatun kanta."

Mai Shari'a Muhammad Tukur ya yanke wa ƴan uwan biyu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 da zaɓin tarar naira 100,000 bayan sun amsa laifinsu kan tuhumar cin amana.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel