Gwamna Umaru Fintiri ya rantsar da sabbin manyan sakatarori 11
- Umar Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya rantsar da sabbin manyan sakatarori guda goma sha daya
- Gwamnan ya ce an zabi sabbin manyan sakatarorin ne bisa cancanta da kwarewar aiki bayan an yi musu jarrabawa
- Dr Edgar Sunday, shugaban ma'aikatan jihar Adamawa, ya hori wadanda aka nada da su gudanar da ayyukansu bisa adalci da daidaito
Gwamnan jihar Adamawa, Umar Fintiri, ya rantsar da sabbin manyan sabbin sakatarori goma sha daya.
Lokacin gudanar da bikin rantsuwa a gidan gwamnatin jiha da ke Yola a ranar Talata, gwamna Fintiri ya ce an yi musu jarrabawar sharar fage don zaɓo waɗanda suka fi cancanta da ƙwarewa wajen gudanar da aiki.
Rantsatsun sakatarorin sun haɗa da Aminu Hammaman Bello, Zainab Umar Adamu, Usman Hamma'ad Mapeo, Muhammad Dabo, da Dorathy Nyanole Augustine.
KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
Sauran sun haɗar da Gajere Japhet Ajiya, Saso Benson Ali, Felicia Jatau Bitrus, Bello Hamman Diram, Isuwa Ksabiya Misau da Ali Aggriey Bechur.
Gwamna Fintiri ya tayasu murnar zama zakaru cikin waɗanda suka zauna jarrabawar wanda hakan ya nun ƙwazo da ƙwarewarsu, ya ce gwamnatinsa nada aniyar farfaɗo da darajar aikin gwamnati.
KARANTA: Majalisa ta amince da bukatar Buhari ta sakin N148bn a matsayin biyan bashi ga wasu jihohi hudu
Ya ce wannan shine dalilin da yasa gwamnatinsa ta kawo sauye sauye a ɗaukar aiki saboda a tabbatar ba'a yi muna-muna ba, saboda kowanne ɗan jihar Adamawa ya samu dama.
Shugaban ma'aikatan jihar Adamawa, Dr Edgar Sunday wanda ya yi wa sabbin sakatorin iso, ya horesu kan su gudanar da ayyukansu bisa adalci da daidaito, sannan su fuskanci duk wani kalubale da ya tunkaro su.
A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta ce gwamnati Shugaba Muhammad Buhari ta gaza yin kataɓus don kawo ƙarshen matsalar tsaron arewacin Najeriya.
NEF ta zargi gwamnatin Buhari da yin burus tare da nuna halin ko in kula ga al-ummar yankin Arewa.
Kakakin ƙungiyar Dattijan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar kunkuru wajen aikin babban titin da ya haɗa jihohin Abuja, Kaduna da Kano.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng