'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun kashe mutum biyu

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun kashe mutum biyu

- Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da mutuwar wasu mutum biyu

- Aruwan ya ce 'yan bindigan da jami'an tsaro suka fatattaka ne yayin da suka yi yunkurin kaiwa matafiya hari a hanyar Kaduna zuwa Abuja suka kai harin

- Baya ga mutum biyu da 'yan bindigan suka kashe sun kuma raunta wasu mutane biyu a garin na Maigiginya

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu a garin Maigiginya da ke karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

An kai harin ne misalin karfe uku na daren ranar Talata kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakayya sunansa sabioda tsaro ya ce 'yan bindigan sun raunta mutane biyu kafin su tsere.

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe mutane biyu a Kaduna. Hoto @GovKaduna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Wadanda aka kashe sunansu Nasiru Yahaya da Isah Bature. Wadanda aka raunta kuma sune Magaji Goma da Zurkhalaini Alhassan.

"Yan bindigan sun kuma sace kayayyakin abinci.

Kwamishinan Tsaron cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da afkuwar harin da kashe mutanen biyu.

Acewarsa, 'yan bindigan da suka kai hari a kauyen suna hanyarsu na tserewa bayan jami'an tsaro sun dakile harin da suka yi yunkurin kaiwa a babban titin Kaduna zuwa Abuja a daren ranar Litinin.

KU KARANTA: Gandirebobi da 'yan acaba sunyi rikici a Agodi

"An sanar da gwamnatin Jihar cewa dakarun atisayen Operation Thunder Strike a daren ranar Litinin sun yi nasarar dakile harin 'yan bindiga a babban titin Kaduna zuwa Zaria.

"Yan bindigan sun bullo a kusa da bututun man fetur da ke unguwar Kakau da nufin kai wa matfiya hari inda dakarun sojoji suka tare su suka fattatake su," in ji Aruwan.

Aruwan ya tabbatar da rasuwar mutane biyun a garin Maigiginya da ke karamar hukumar Igabi da suka sauran mutum biyu da suka jikkata.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel