Likafa ta cigaba: Aisha Yesufu ta shiga jerin jadawalin BBC na mata 100 masu faɗa aji na duniya

Likafa ta cigaba: Aisha Yesufu ta shiga jerin jadawalin BBC na mata 100 masu faɗa aji na duniya

- Gidan jaridar BBC ma su yada labarai sun fitar da jadawalin mata masu a fada a ji na duniya na shekarar 2020

- Sunan 'yar gwagwarmaya, 'yar asalin jihar Kano, Aisha Yesufu, ya bayyana a cikin jerin sunayen

- A kwanakin baya ne wani lauya ya shigar da karar Aisha Yesufu da sauran wasu 'yan Nigeria da suka taka rawa wajen zangar-zangar EndSARS

Ƴar gwagwarmayar Najeriya kuma shugabar ƙungiyar kiran #Bring back our girls; ta ta gwagarmayar 'yammatan Chibok, Aisha Yesufu, ta shiga jadawalin shaharrarrun mata masu faɗa aji 100 na duniya na shekarar 2020.

Sunan fitacciyar ƴar gwagwarmayar yazo a jere da na Sanna Marin wacce ta jagoranci haɗakar gwamnatin mata zalla, Michelle Yeoh; tauraruwar sabuwar halittar Marvel, da Sarah Gilbert; wacce ta jagoranci binciken allurar rigakafin Korona a jami'ar Oxford, tare da Jane Fonda; ƴar gwagwarmayar sauyin yanayi kuma jaruma.

Wacece Aisha Yesufu?

Aisha Yesufu haifaffiyar jihar Kano ce, an haifeta 12 ga watan Disamba na shekarar 1974.

KARANTA: Majalisa ta amince da bukatar Buhari ta sakin N148bn a matsayin biyan bashi ga wasu jihohi hudu

'Yar gwagwarmayar zamantakewa da siyasa, kuma jagora a ƙungiyar #Bring back our girls, ƙungiyar da ta jawo hankalin duniya kan sace yara mata ƙanana sama da 200 a wata makarantar Sakandiren 'yammaata a Chibok, jihar Borno, a ranar 14 ga watan Afrilu, 2014, wanda ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram suka ƙwamushe su.

Likafa ta cigaba: Aisha Yesufu ta shiga jerin jadawalin BBC na mata 100 masu faɗa aji na duniya
Likafa ta cigaba: Aisha Yesufu ta shiga jerin jadawalin BBC na mata 100 masu faɗa aji na duniya
Asali: UGC

Aisha Yesufu ta na kan gaba a tafiyar kawo ƙarshen rundunar SARS#EndSARS, wani kira da ya jawo hankalin duniya kan kitimurmurar da sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami(SARS) na rundunar ƴan sanda ke aikatawa.

KARANTA: Bidiyo: Wani jarumin mutum ya kwato karensa daga bakin Guzan da ya so yin kalaci da shi

Iyayen Aisha dai ƴan asalun jihar Edo ne, amma ita tashinta da girmanta duk a Kano ne,ta sha bayyana irin wahalhalu da ƙalubalen da ta fuskanta saboda kasancewarta ita kaɗai ce ɗiya mace wadda ta taso cikin maza.

A jawabinta tana cewa, "Lokacin da nake da shekaru 11 a duniya, banda ƙawa ko ɗaya, saboda duka an aurar da su, amma ni ina son na yi ilimi in bar ƙauye."

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube yayin mayar da martani ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda 'ta yi uwa, ta yi makarbiya' a zanga-zangar ENDSARS.

Aisha, wacce sunanta ya kara karada gari saboda zanga-zangar ENDSARS, ta ce ko kadan hakan bai taba damunta ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng