Bidiyo: Wani jarumin mutum ya kwato karensa daga bakin Guzan da ya so yin kalaci da shi

Bidiyo: Wani jarumin mutum ya kwato karensa daga bakin Guzan da ya so yin kalaci da shi

- Wani mutum ya nuna bajinta da jarumta domin ceto rayuwar wani karamin karensa da guza ya kusa yin kalaci da shi

- Mutumin ya yi allan baku, ya fada cikin tafkin ruwa tare da shake mukamukin Guzan da ya kama karensa

- Sai dai, mutumin ya ce; ba zai kashe Guzan ba saboda ya na rayuwa ne a gurbinsa, shi dai ya yi sa'a ya ceci karensa

Wani mutum mamallakin wani kare za'a iya kiransa da "jarumin duniya" bayan yayi tsalle, yayi allon baku cikin ruwa, ya yi faɗa da wani guza da yake shirin hallaka ɗan kwuikwuyonsa.

Wani bidiyo da ya karaɗe duniya ya nuna yadda mutumin yake faɗa da guza da hannuwansa don ceto ɗan kwuikwuyonsa da guzan ya yi wuf da shi zuwa cikin ruwa a Florida ta kasar Amurka.

KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun afka gidan dan majalisar wakilai, sun sace mutum biyu

Richard Wilbanks, daga Florida, Amurka, an gano shi a wani bidiyo yayin da ya daka tsalle ya fada cikin wani ruwa mara zurfi yana ta faman faɗa da guzan don ceto ɗan ƙaramin karen nasa.

Bidiyo: Wani jarumin mutum ya kwato karensa daga bakin Guzan da ya so yin kalaci da shi
Bidiyo: Wani jarumin mutum ya kwato karensa daga bakin Guzan da ya so yin kalaci da shi
Asali: UGC

A wani bidiyo mai ban mamaki, mutumin ya yi tsallan baɗake cikin kududdufi, ya shake muƙamuƙin guzan, sannan ya janyo shi daga cikin ruwan a yayin da ya ke riƙe da karen nasa mai suna Gunner.

KARANTA: Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi

Yana gurnani cikin fushi, ya take kan guzar ya zare karen nasa daga bakin guzar, abin mamakin kuma shine ya samu ya tsira ba tare da jin wani mummunan ciwo ba.

Bidiyon, wanda ma'aikatar kula da dabbobin daji ta Florida ta watsa shi, ya ƙare lokacin Richard yana tsaye kyam a cikin ruwan.

Da yake bayani akan al-ajabin da ya afku, ya gayawa gidan talabijin na CNN "muna tafiya ta gefen ruwa sai kawai guzan ya yi tsalle daga ruwan kamar an harbo shi.

"Ban taɓa tunanin guza zai iya wannan saurin ba. Hanzarinsa yayi yawa."

"Karen mai suna Gunner yaji ciwo yayin harin, amma abin godiyar shine ya tsallake rijiya da baya," a cewarsa.

Richard ya ce bai yi tunanin lafiyarsa ba kwata kwata, ya ce yana ɗaukan karnukansa tamkar "ƴaƴansa" kuma zai iya sallama komai akansu.

"Karen ya ji ciwo kaɗan, ni kuma ya ciji hannuna"a cewarsa.

Richard da matarsa, Louise Wilibanks, yanzu haka suna tafiya da Gunner da tazarar ƙafa goma tsakaninsu da ruwan, kuma sun ce basa son su a hallaka guzan tunda sun ce yana rayuwarsa ne a gurbinsa.

A wani labarin kwatankwacin irin wannan da Legit.ng ta wallafa, wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwar zamani ya nuna yadda wata amarya ta hana angonta sumbatarta saboda kar ya ɓata mata kwalliyar bikinta.

A cikin faifan bidiyon, amaryar da angonta suna shirin shiga coci cikin shigar fararen kayan ɗaura aurensa, sai suka yanke shawarar ɗaukar hotuna kafin su bar wurin.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: