A haramta wa yaran masu riƙe da muƙaman siyasa zuwa karatu ƙasashen waje, in ji ASUU

A haramta wa yaran masu riƙe da muƙaman siyasa zuwa karatu ƙasashen waje, in ji ASUU

- Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ta bada shawarwari kan yadda za a kawo karshen yawan yaji aikin yi

- Kungiyar ta ce ya zama dole a kafa doka da zata hana masu rike da mukaman siyasa da yaransu zuwa kasashen waje karatu ko asibitoci neman magani

- Ta kuma ce idan ba gwamnati ta canja halinta ta mayarda hankali wurin gina ilimi a kasar ba da wuya a kawo karshen yajin aikin

Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta ce hanya guda da za a magance yawan yajin aiki ita ce kafa doka da zata haramtawa masu rike da mukamai a gwamnati tura yaransu karatu kasashen waje.

Shugaban ƙungiyar na shiyya, Farfesa Olufayo Olu-Olu, cikin wata sanarwa ya ce hakan zai taimaka wurin gina ɓangaren ilimi a ƙasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A haramta wa yaran masu riƙe da muƙaman siyasa zuwa karatu ƙasashen waje, in ji ASUU
A haramta wa yaran masu riƙe da muƙaman siyasa zuwa karatu ƙasashen waje, in ji ASUU. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

"Masu mulki da abokansu duk yaransu na karatu a ƙasashen ƙetare, don haka ba su damu da kawo ƙarshen yajin aikin ASUU ba tunda mulkin ya zama sana'a ne a wurinsu ba yi wa al'umma hidima ba.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

"Idan ba mun kafa doka kan wasu abubuwa biyu ba, ba zamu rabu da wannan matsalar ba - na farko, dokar da zata tilastawa masu riƙe da muƙaman siyasa da yaransu yin karatu daga frimari har makarantun gaba da sakandare a Najeriya.

"Na biyu, doka ta zata haramtawa masu riƙe da mukaman siyasa da iyalansu zuwa kasashe waje neman magani. Idan an kafa wannan dokokin biyu, da yiwuwar mu fara ganin ƙarshen yajin aikin ASUU a ƙasar nan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara

"Idan har gwamnati bata yi abinda ya dace ba (an saki kudaden don gina makarantun mu, an biya allawus ɗin mu da wasu sauran abubuwa) zamu cigaba da wannan gwagwarmayar," a cewar wani bangare na sanarwar.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel