A cikin shekaru biyar, Najeriya ta samu $206bn daga man fetur - OPEC
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, ta ce Najeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce fitar da man fetur a nahiyar Afrika, ta samu dala biliyan 206.06 na kudin shiga ta hanyar fitar da mai a shekaru biyar da suka gabata.
A kididdigar alkaluman shekara-shekara da OPEC ta fitar a ranar Litinin, ta ce a bara Najeriya ita ce kasa ta biyar cikin jerin kasashen duniya da suka fi kowanne samun kudin shiga ta hanyar fitar da man fetur.
Jerin kasashen biyar da a bara suka samu tarin dukiya ta hanyar fitar da danyen mai sun hadar da;
Saudiyya - ($202.37bn)
Iraq - ($80.03bn)
Kuwait - ($52.43bn)
Hadaddiyar Daular Larabawa U.A.E - ($49.64bn)
Najeriya - ($45.11bn)
Alkaluman da OPEC ta fitar sun bayyana daki-daki adadin kudin shiga da Najeriya ta samu a kowace shekara cikin shekaru biyar da suka gabata a baya-bayan nan.
Ga jerin kudin shiga da Najeriya ta samu ta hanyar fitar da danyen mai daga shekarar 2015 zuwa bara kamar haka:
2019 - $45.11bn
2018 - $54.51bn
2017 - $37.98bn
2016 - $27.29bn
2015 - $41.17bn
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, fitar da danyen man fetur da Najeriya ke yi zuwa nahiyar Turai a kullum ya yi kasa a bara idan an kwatanta da shekarar 2018.
KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na amince a sayar da kadarar Najeriya ga kamfanin da ake tuhuma da laifin zamba - Malami
Rahotanni sun nuna cewa, a bara Najeriya ta rika fitar da gangunan danyen man fetur 680,600 a kullum zuwa nahiyyar Turai sabanin ganguna miliyan 1.06 da suka rika fita a shekarar 2018.
Mambobin OPEC 13 sun samu ragi na kashi 18.4 cikin dari na kudaden shiga da suka samu a shekarar 2019 ta hanyar fitar da danyen mai zuwa kasuwannin duniya.
Hakan ya biyo bayan faduwar farashi da danyen man ya yi daga dala 71 duk ganga a 2018 zuwa dala 64 duk ganga a 2019 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Amurka ya nuna.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng