Makiyaya sun sake kutsawa gidan gonar Falae, sun fatattaki ma'aikata

Makiyaya sun sake kutsawa gidan gonar Falae, sun fatattaki ma'aikata

- Tsohon ministan kudi, Olu Falae, ya yi korafi a kan yadda makiyaya su ka taso gonarsa dake jihar Ondo gaba

- A cewarsa, makiyayan sun kara shiga gonarsa, inda suka saci hatsi masu kimar miliyoyi sannan suka lalata wasu

- Sun kuma je da miyagun makamai, har suka kori masu masa aiki a gonar sannan suka sace musu kudade da kayan aiki

Tsohon ministan kudi, Olu Falae, ya yi korafi a kan sabon harin da makiyaya suka kai gonarsa da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, Premium times ta wallafa haka.

Falae, wanda tsohon sakataren gwamnatin tarayya ne, ya ce makiyayan sun lalata kuma sun saci hatsi masu kimar miliyoyin nairori a gonarsa.

Ya yi wannan korafin ne a wata takarda da ya gabatar wa da darekta janar na harkokin tsaron jihar Ondo, wanda aka fi sani da Amotekun Corps.

Makiyaya sun sake kutsawa gidan gonar Falae, sun fatattaki ma'aikata
Makiyaya sun sake kutsawa gidan gonar Falae, sun fatattaki ma'aikata. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

A cewarsa, sun kai a kalla shekaru 3 suna kai hari gonarsa. Ya ce ya kai kararsu wurin 'yan sanda da shugaban Miyetti Allah na jihar, amma duk da haka babu abinda ya canja.

"Yan sandan da aka turo gonata sun kori makiyayan, amma washegari bayan sun tafi, makiyayan sun koma gonar ta wa," cewar Falae.

"Sun saci wasu hatsin, sannan suka lalata wadanda suka kasa tafiya dasu.

Sannan sun je gonar da miyagun makamai, inda suka kori duk ma'aikatan da ke gonar, kafin su yi barnar. Daya daga cikin ma'aikatan ya ce ta taga ya tsere bayan makiyayan sun isa gonar.

Ya kara da cewa, sai da suka duba dakunan da ke cikin gonar, suka sace kaya, kudade har da adduna.

KU KARANTA: Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Jami'in hulda da jama'a, Tee Leo-Ikoro, ya ce bai san an kai harin ba, kuma bai tabbatar idan an kai kara ba ko ba a kaiba.

Darekta janar, Adetunji Adeleye, ya tabbatar wa da Premium Times cewa wasikar Falae ta isa wurinsa a ranar Litinin. Kuma ba zai cigaba da tattaunawa a kan lamarin ba, har sai sun karasa bincike. Saboda yawan magana a kai zai iya kawo cikas ga binciken da za su yi.

A wani labari na daban, hankula sun karkata a kan jam'iyyar APC ta jihar Legas a kan zaben 2023, da kuma hanyoyin dakatar da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu.

Duk da dai har yanzu zaben 2023 yana da tazara, jam'iyyar APC ta jihar ta shiga tararrabi a kan yadda masu fadi a ji suka fara nuna kwadayin mulkin jihar Legas, karara. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel