2023: Kokarin kwace karfin ikon Tinubu ya tsananta

2023: Kokarin kwace karfin ikon Tinubu ya tsananta

- Jam'iyyar APC ta jihar Legas ta dauki zafi a kan zaben 2023 na gwamnan jihar

- Duk da dai jam'iyyar PDP ta jihar ta lashi takobin mulkar jihar a 2023

- 'Yan cikin jam'iyyar APC suna ta fitowa fili da sunan adawa da Bola Tinubu

Hankula sun karkata a kan jam'iyyar APC ta jihar Legas a kan zaben 2023, da kuma hanyoyin dakatar da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Duk da dai har yanzu zaben 2023 yana da tazara, jam'iyyar APC ta jihar ta shiga tararrabi a kan yadda masu fadi a ji suka fara nuna kwadayin mulkin jihar Legas, karara.

Ba nuna kwadayin mulkin kawai suka fara ba, suna ta nuna cewa Tinubu bai isa ya dakatar da su ba, duk da matsayinsa na shugaban jam'iyyar a jihar.

2023: Kokarin kwace karfin ikon Tinubu ya tsananta
2023: Kokarin kwace karfin ikon Tinubu ya tsananta. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

Duk da dai, jam'iyyar adawa ta PDP ta kaddamar da kamfen, wanda ta kira da 'O toge Lagos' don kawo karshen mulkin Tinubu a 2023, sannan APC ta lashi takobin ba za ta bar PDP ta maye gurbinta ba.

KU KARANTA: Dogarin babban mutum a Najeriya ya harbe mutum 1 tare da yin mummunan rauni ga wani

Yanzu haka, jam'iyyar APC tana gwagwarmaya da jam'iyyar PDP, ga kuma wasu masu adawa da ita, 'yan cikin jam'iyyar.

A watan da ya gabata, tsohon kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Dr Abdulhakeem Abdullateef, ya fita daga jam'iyyar bayan ya bayyana burinsa na tsayawa takara a 2023.

Bayan ya sanar da hakan, an sallame shi daga mukaminsa na hadimin kakakin majalisar jihar, Mudasiru Obasa.

Amma ya janye burinsa cikin awanni 24 bayan ya tattauna da wasu shugabannin jam'iyyar, sannan wasu sun ce ya bar maganar tsayawa takarar.

KU KARANTA: Zulum ya magantu a kan harin da ake rade-radin 'yan Boko Haram sun kai masa

Bayan watanni 2 kenan da al'amarin ya faru, wani jagaba na jam'iyyar, Olajide Adediran, ya fito makon da ya gabata, ya sanar da burinsa a zaben 2023.

Ya ce Tinubu bai isa ya dakatar da shi daga tsayawa takara ba, duk da kowa yasan kut-da-kut Adediran yake da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.

Ya ce ba shi da tabbacin Tinubu zai amince da burin nasa, amma hakan ba zai dakatar dashi ba.

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Mallam Uba Sani, ya alakanta hare-hare da garkuwa da mutanen da ake yi a jihar Kaduna da mummunan yanayin titunan gwamnatin tarayya na jihar, musamman titin Abuja zuwa Kaduna har Zaria.

Mai kawo wa Legit.ng rahotonni na Kaduna, Nasir Dambatta, ya tabbatar da yadda sanatan ya bayyana abinda yake zuciyarsa a kan gyare-gyaren da ya kamata a yi a jihar, a taron masu ruwa da tsaki da aka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng