Da duminsa: Masu hidmar kasa 138 sun harbu da cutar korona

Da duminsa: Masu hidmar kasa 138 sun harbu da cutar korona

- A kalla masu bautar kasa 138 suka kamu da cutar COVID-19

- Darekta janar na NCDC ne ya bayyana hakan a ranar Litinin

- A cewarsa, NCDC tana aiki tukuru a kan wannan al'amarin

A kalla masu bautar kasa 138 ne suka kamu da cutar COVID-19. Chikwe Ihekweazu, darekta janar na NCDC ne ya sanar da hakan, a lokacin da yana sanar da jami'an kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa.

A cewarsa, NCDC tana iyakar kokarin ganin ta karasa bude duk wasu sansanin masu bautar kasa da ke cikin kasar nan, The Cable ta wallafa.

Ya ce wadanda suka harbu da cutar na daga cikin masu digiri 34,785 da kuma ma'aikatan sansanin da aka yi wa gwaji a makon da ya gabata ne.

Ya ce hakan yana nuna kashi 0.4 ne ke dauke da cutar wanda a kalla ana iya samun mutum daya a cikin kowanne mutm 200.

Da duminsa: Masu hidmar kasa 138 sun harbu da cutar korona
Da duminsa: Masu hidmar kasa 138 sun harbu da cutar korona. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Ya kara da jaddada cewa an samu manyan nasarori wurin bude sansanin 'yan bautan kasa kuma ba a ba ko mutum daya mai dauke da cutar damar shiga sansanin ba.

"Wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar ana musu magani daga gida ne ko kuma cibiyar killacewa, hakan ya dogara da yanayin karfin cutar a jikinsu," yace.

Shugaba a PTF, Dr Sani Aliyu, ya yi kira ga makarantu da su aike da dalibi gida matukar sun lura yana da wata cuta ta numfashi domin guje wa yaduwar mugunyar cutar korona.

Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya ce gwamnati a cikin makon nan za ta kaddamar da kwamitin kasa na mutum 18 da za su tabbatar da samuwar riga-kafin cutar korona da wadatarsa a cikin kasar nan.

KU KARANTA: Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

A wani labari na daban, ana kyautata zaton tituna za su kara cunkoso sakamakon yadda mazauna kusa da wuraren jiragen ruwa suke cike da tsoro, bayan wasu wadanda ake zargin bata-gari ne sun kai wa 'yan kwamitin samar da tsaro na fadar shugaban kasa hari a Apapa.

Kamar yadda bayanai su ka kammala, al'amarin ya faru ne a wuraren gate na biyu, na TinCan Island Port, dake Apapa, cikin kwanakin karshen mako, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel