'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP a Katsina

'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP a Katsina

- Allah ya yi wa Alhaji Lawal Dako, shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Sabuwa a Katsina rasu

- Alhaji Lawal Dako ya rasu ne sakamakon harbinsa da 'yan bindiga suka yi yayin wani hari a ranar 8 ga watan Nuwamban 2020

- Tun bayan harin, an marigayin ya dinga jinya a kuma ya rasu a Asibitin Koyarwa ta Ahmadu Bello Zaria a ranar 20 ga watan Nuwamba

'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, Alhaji Lawal Dako.

A cewar Katsina Post, yan bindiga sun harbe Lawal Dako ne a ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2020 amma ya rasu a ranar 20 ga watan Nuwamba sakamakon raunin da ya samu yayin harin da suka kai masa.

'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP a Katsina
'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP a Katsina. Hoto: middleeastpress
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Marigayin ya rasu na Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan bindiga a Najeriya.

KU KARANTA: An aikewa masu nadin sarki 4 takardar tuhuma kan rashin halartar taron naɗin sabon sarkin Zazzau

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon saka harajin.

Wani jigo a kungiyar wanda aka fi sani da Godfirst ya ce suna shirye shiryen yadda zasu zauna da masu alhakin karbar kudin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164