An kama mutum biyu bisa zargin cin babbakakken naman 'yan sanda

An kama mutum biyu bisa zargin cin babbakakken naman 'yan sanda

- Ana zargin wasu mutane biyu da cin babbakakken naman yan sanda a Ibadan babban birnin jihar Oyo

- Duka su biyun sun karyata zargin yayin da kowa yake alakanta laifin ga dan uwansa

- 'Yan sandan dai an girke su ranar 22 ga Oktoba don kula da masu zanga zangar #endsars lokacin da suka gamu da ajalinsu

Rundunar 'yan sandan Jihar Oyo ta tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da cin naman 'yan sandan da aka kona lokacin zanga zangar EndSARS.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ranar Asabar a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

An kama mutum biyu bisa zargin cin babbakakken naman 'yan sanda
An kama mutum biyu bisa zargin cin babbakakken naman 'yan sanda. Hoto @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Wanda ake zargin, wata mata mai shekara 34 da kuma wani dattijo mai shekaru 43, an mika su ga cibiyar bincike ta 'Force Intelligence Bureau' a hedikwatar hukumar da ke Abuja don fadada bincike, a cewar sa.

Yar shekara 34, an zarge ta da cin sassan daya daga cikin yan sanda da aka kona, lamarin da ta karya duk da tana wajen da abun ya faru, ta ce dayan da ake zargi dai ya bata wasu sassa ta ajiye masa.

KU KARANTA: Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Dan shekara 43, shima bai karyata kasancewar sa a wajen da abin ya faru ba, amma yace matar ce ta dauki wasu sassa kuma ta roki ya bata tsumman da zata daure a ciki.

'Yan sandan dai an girke su ne don kula da kula da masu zanga zangar EndSARS ranar 22 ga Oktoba lokacin da suka gamu da ajalinsu.

A wani labarin, an aike wa hudu daga cikin masu nadin sarki biyar na masarautar Zazzau takardar neman jin ba'asi saboda rashin hallartar taron nadin sabon sarkin Zazzau kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Taron nadin wanda Kwamishinan kananan hukumomi ya jagoranta a ofishin sa a shirye shiryen bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bammali wanda ya gudana a ranar ga watan Nuwamba 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel