An aikewa masu nadin sarki 4 takardar tuhuma kan rashin halartar taron naɗin sabon sarkin Zazzau

An aikewa masu nadin sarki 4 takardar tuhuma kan rashin halartar taron naɗin sabon sarkin Zazzau

- An aikewa 'yan majalisar sarki takardar tuhuma mai taken "rashin halartar taron tattaunawa da ma'aikatar kananan hukumomi ta shirya - tuhuma"

- Daga cikin wandanda aka aikewa takardar akwai limamin Zazzau, Wazirin Zazzau, Limamin Kona da Makama Karami kan rashin halartar wani taro da aka yi kan shirin bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau

- An bada awa 48 ga wanda suka karbi tuhumar da suyi bayani, sai dai wani rahoto ya nuna wasu daga cikin masu zaben sarkin, basa jin dadin yadda al'amura ke gudana a masarautar

An aike wa hudu daga cikin masu nadin sarki biyar na masarautar Zazzau takardar neman jin ba'asi saboda rashin hallartar taron nadin sabon sarkin Zazzau kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Taron nadin wanda Kwamishinan kananan hukumomi ya jagoranta a ofishin sa a shirye shiryen bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bammali wanda ya gudana a ranar ga watan Nuwamba 2020.

An aikewa yan majalisar sarki 4 takardar tuhuma bisa rashin halartar taron nadin sabon sarkin Zazzau
An aikewa yan majalisar sarki 4 takardar tuhuma bisa rashin halartar taron nadin sabon sarkin Zazzau. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar

Wanda aka aikewa da takardar sune Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu, Limamin Kona Alhaji Sani Aliyu, Limamin Zazzau Alhaji Dalhat Kasimu da Makama Karami Alhaji Mahmoud Abbas.

Baza a gano cewa ko an aikewa cikon na biyar din masu zaben sarkin, Fagachin Zazzau makamanciyar wannan tuhuma ba.

Taken takardar tuhumar shine: "rashin halartar taron tattaunawa da ma'aikatar kananan hukumomi ta shirya- tuhuma" mai lambobin shaida MLGCA/36/Vol:Vi/1059 da kwanan wata 30 ga Oktoba 2020 dauke da sa hannun Musa Adamu, babban sakataren ma'aikatar kananan hukumomi.

KU KARANTA: Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito

Cikin kunshin tuhumar "zaku iya tunawa ranar Juma'a, 30 ga Oktoban 2020, an gayyace ku taro da mai girma kwamishinan kananan hukumomi ya shirya a ofishin sa amma kuka gaza halarta.

"Saboda haka, an baku awa 48 kuyi bayanin dalilin da yasa baza a dauki mataki akan ku ba."

Wasu daga cikin masu zaben sarkin, a cewar wani rahoto, basa jin dadin yadda al'amura ke gudana a masarautar.

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164