Ku manta da kibar albashinmu, ku kalli nagarta da muhimmancin aikinmu; Lawan ga 'yan Nigeria

Ku manta da kibar albashinmu, ku kalli nagarta da muhimmancin aikinmu; Lawan ga 'yan Nigeria

- Sanata Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattijai ya bukaci 'yan Nigeria su bawa aikin 'yan majalisa muhimmanci ba albashinsu ba

- 'Yan Nigeria manya da kanana sun sha yin korafi a kan 'nauyin' albashin 'yan majalisa da babu abinda suke sai cin bulus

- Wasu da dama sun sha yin kiran a soke daya daga cikin majalisun kasar nan domin kudi kawai suke ci ba tare da yin wani aiki ba

Shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya roƙi ƴan Najeriya da su buƙaci nagarta da kuma tabbatar da ƴan majalisu ba zanan ɗumama kujera suke yi ba maimakon tambayar yawan gwagwaɓan albashin da suke karɓa.

Yayi wannan kira ne ranar Juma'a lokacin da yake magana a wurin ritayar wasu manyan ma'aikata na Majalisar Dattijai da kuma ɓangaren aikin majalisar a Abuja.

Ahmad Lawan ya ce, kuɗaɗen da majalisar take karɓa ba ya isar su, sakamakon haka, da yawa daga cikin "masu zartar da dokar suna gwagwarmaya don yin abubuwa da kansu."

KARANTA: A kama shi duk inda aka gan shi; umarnin kotu bayan ta janye belin Abdulrasheed Maina

"Ba wai ina goyon bayan a bamu abin da ya wuce kima bane, amma abin da muke dashi a halin yanzu ba isarmu yake ba, sannan zaka sami ƴan majalisu suna gwargwarmarya don ɗaukar ɗawainiyar kansu.Wanda hakan ba shine abin da yafi kamatar mu ba.

Ku manta da kibar albashinmu, ku kalli nagarta da muhimmancin aikinmu; Lawan ga 'yan Nigeria
Ku manta da kibar albashinmu, ku kalli nagarta da muhimmancin aikinmu; Ahmed Lawan ga 'yan Nigeria @Thecable
Asali: Facebook

"Shin zamu iya muhawarar amfanin majalisar ƙasar maimakon magana akan gwaggwaɓan albashin su? Ina gwaggwaɓan albashin yake?

"Kamata yayi muke duba darajar aiki ba kuɗinsa ba."

"Saboda haka maimakon ace kullum muhawararmu akan gwaggwaɓan albashi yan majalisa take, ya fi dacewa ake duba abin da ya kamata muyi da wanda bai kamata ba, ko kuke tambaya akan abun da ya kamata mu yi da bada shawarwarinku, ba wai ku ke cewa a rufe majalisar wakilai ko dattijai ba. Shin kun san illar yin hakan? Ahmad Lawan ya tambaya."

KARANTA: Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa

Lawan, ya yi ƙorafin cewa majalisa tana samun ƙasa da kaso ɗaya 1% na kasafin ƙasa, a saboda haka bai kamata ma ake batun yanke musu albashin ba.

"A kasafin kuɗin da ya haura sama da Naira tiriliyan ₦13, Majalisa tana samun kasafin Naira biliyan ₦125 zuwa ₦128. Kaso nawa acikin kasafin? Kason da bai kai ko kashi ɗaya ba. To ina sauran kashi casa'in da tara 99%?

"Duk da haka, maimakon ku tsaya duba hanyoyin da za'a bi wajen amfani da kuɗin ko ku kalli amfanin kuɗaɗen ga jama'ar Najeriya, sai kuyita cewa a yanke mana kuɗaɗe, abin ai sai ya yi yawa, bai dace ba sam," a cewarsa.

Malam Lawan yace zai fi yi wa ƴan Najeriya suke muhawara akan muhimmancinmu maimakon kiran a soke mu.

Malam ya ƙalubalanci ƴan Najeriya da su canja ƴan majalisun wannan lokacin a zaɓen 2023 ta hanyar ƙin sake zaɓarsu matukar sun gaji da ganin fuskokinsu.

A ranar Talata, 17 ga wata, ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa majalisa ta aika takardar gayyata zuwa ga shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC) da kuma gwamnan babban bankin kasa (CBN) domin su yi bayani a kan batan dabon wasu kudade masu nauyin gaske.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel