An kama ɗan shekara 19 da ake zargi da fashi da bindigar roba a Legas

An kama ɗan shekara 19 da ake zargi da fashi da bindigar roba a Legas

- Dubun wani matashi mai shekaru 19 da haihuwa da dan fashi da makami ta cika a birnin Legas

- Ƴan sanda sun kama Ajayi Lateef da bindigar roba a Victoria Island bayan ƴan ƙungiyarsu sunyi fashi

- Kwamishinan rundunar ƴan sandan Jihar Legas ya bada umurnin a aike da wanda ake zargin sashin binciken manyan laifuka wato CID

Rundunar ƴan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama wani matashi ɗan shekara 19, Ajayi Lateef kan zargin fashi da makami.

An kama shi da bindigar roba bayan ƴan ƙungiyarsu sun yi wa wani mai adaidaita sahu fashi a Victoria Island misalin ƙarfe 1 na dare kamar yadda LIB ta ruwaito.

An kama ɗan shekara 19 da ake zargi da fashi da bindigar roba a Legas
An kama ɗan shekara 19 da ake zargi da fashi da bindigar roba a Legas. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

An kama ɗan shekara 19 da ake zargi da fashi da bindigar roba a Legas
An kama ɗan shekara 19 da ake zargi da fashi da bindigar roba a Legas. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: An yanke wa mutumin da ya datse kan dansa hukuncin kisa a Adamawa

Kakakin ƴan sandan jihar Legas, Olumuyiwa Adejobi ya ce kwamishinan ƴan sandan Jihar, Hakeem Odumosu ya bada umurnin a mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na CID Panti don zurfafa bincike.

Yan sandan na kyautata zaton bayanan da za a samu daga gare shi zai taimaka wurin kamo sauran 'yan kungiyar da suke fashin da makami tare.

A wani labarin daban Legit.ng ta wallafa, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jigawa, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da kama ta ya ce ana cigaba da bincike don gano sauran wadanda ake zargin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel