Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa

Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa

- Nan da makonni biyu zamu gama kanikancin kasafin kudin 2021, Sanata Barau Jibrin

- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin gaban majalisa a watan Oktoba

- Sanata Ahmed Lawan ya yi alkawarin zasu kammala aiki kan kasafin kudin kafin karshen shekara

Kwamitin majalisar dattawa kan lissafe-lissafen kasafin kudi a ranar Laraba ta yi alkawatin gabatar da kammalallen daftarin kasafin 2021 a zauren majalisa ranar 3 ga Disamba.

Shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana hakan bayan shugabannin wasu kwamitoci suka gabatar da rahotanninsu,

Barau ya bayyanawa yan jarida cewa bayan gabatar da kasafin a zauren majalisar, Sanatocin zasu gaggauta amincewa da ita, The Punch ta ruwaito.

Yace: "Muna da jadawalinmu; muna son gabatarwa nan zuwa ranar 3 ga Disamba, 2020. Zamu gabatar da daftarin kasafin kudin 2021 idan Allah ya yarda."

Yayinda aka tambayeshi shin kwamitin za tayi tsokaci kan cire wasu ma'aikatu daga cikin kasafin, shugaban kwamitin yace duka wannan ba matsala bane,

Ya ce kwamitin za ta magance duk wani matsala.

KU KARANTA: FEC ta amince da N13.08trn na kasafin kudin 2021

Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa
Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa Hoto: @MaiWayaIbrahim2
Asali: Twitter

Kasafin kudin shekarar 2021, kamar yadda Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya tiriliyan N13.08 tiriliyan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ma'aikatan gwamnatin da aka yiwa rijista a manhajar biyan albashi ta IPPIS kadai zasu samu albashi a shekarar 2021.

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU yanzu haka tana yajin aiki kuma ta lashi takobin cewa ba zata amince da manhajar IPPIS ba.

KU KARANTA: FG ta saki N5.2bn domin ginin gidajen 'yan gudun hijira, Zulum

A kan kasafin kudin kuma, sakataren din-din-din fadar shugaban kasa, Tjjani Umar, ya ce kudi bilyan 1.3 da aka tanadarwa asibitin fadar shugaban kasa a kasafin 2021 ya yi kadan.

Ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai ranar Alhamis bayan kare kasafin kudin 2021 da ma'aikatarsa ta gabatar gaban kwamitin harkokin gwamnati, Punch ta ruwaito.

Umar wanda yayi alkawarin tabbatar da cewa shugaban kasa, iyalansa da manyan jami'an gwamnati sun samu isasshen kayan lura da lafiya idan aka amince da kudin.

"Kudi N1.3bn gaskiya ya yi kadan idan ka hada da kudin da muka bukata, kudi, " yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng