FG ta saki N5.2bn domin ginin gidajen 'yan gudun hijira, Zulum
- Gwamnan jihar Borno ya yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari saboda kokarinsa a kan jihar Borno
- Gwamna Babagana Zulum, ya ce Buhari ya yi gaggawar sakin kudin da jiharsa ta nema a wurinsa
- Ta nemi kudade ne don ginawa 'yan gudun hijira miliyan 1.7 gidaje 10,000, wanda yanzu haka an gama
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi wata magana yayin da yake zagaye anguwannin gidajen 'yan gudun hijira 1000 a waje-wajen jihar.
Inda yace kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar don gina gidaje 10,000 na a kalla 'yan gudun hijira miliyan 1.7 da ya kamata a ce sun koma anguwanninsu.
KU KARANTA: Lalata da masu neman fasfoti: Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da ma'aikaci
'Yan gudun hijiran da suka dawo yanzu haka sun yada zango ne a sansanin gudun hijira da ke Maiduguri, Dikwa, Monguno, Dolori da kuma wasu anguwanni masu makwabtaka da kasar Kamaru.
Zulum ya ce gwamnatin jiharsa ta nemi kudi daga hannun gwamnatin tarayya, a kan ginawa masu gudun hijira gidaje, kuma an basu, The Punch ta wallafa.
Gwamnan, ya yaba wa shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarinsa da jajircewarsa a kan sakin kudin gine-ginen gidajen 'yan gudun hijira miliyan 1.7, wadanda 'yan boko haram suka lalata.
KU KARANTA: Mallake kadarorin miji da matar aure ta bayyana ta yi, ya janyo cece-kuce
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, kuma sanata mai wakiltar yankin Imo ta yamma, Rochas Okorocha, ya nuna kwadayinsa a kan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Tsohon gwamnan, wanda yayi maganar yayin da wata kungiya wacce ta kira kanta da sunan 'Igbos for Rochas 2023 President', wato kungiya mai marawa Rochas bayan shugabancin kasa a 2023, wacce Jeff Nwaoha ya jagoranta, daga jihohi 5 na yankin kudu maso gabas, tace lokacin da kabilar Ibo za ta samar da shugaban kasar Najeriya yayi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng