FEC ta amince da N13.08trn na kasafin kudin 2021

FEC ta amince da N13.08trn na kasafin kudin 2021

- Majalisar zartarwar tarayya ta Najeriya ta amince da fitar da tiriliyan N13.08 a matsayin kasafin kudin 2021

- Ministar kudi, kasafi da tsari, Zainab Shamsuna Ahmed ce ta sanar da manema labaran gidan gwamnati

- Ta yi musu bayanin ne bayan kammala taron majalisar wanda ya samu halartar Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta a taronta na yau Laraba, ta amince da fitar da tiriliyan N13.08 a matsayin kasafin shekarar 2021.

Ministan kudi, kasafi da tsarin kasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a wani taro na manema labarai akan abinda majalisar zartarwar ta zartar a taron da aka yi a wani dakin taro dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Hajiya Zainab tare da Minsitan yada labarai da al'adu, Lai Muhammed; karamin Ministan kasafi, tsari da tattali, Clement Agba da darakta janar na ofishin kasafin kasa, Ben Akabueze ne suka yi bayanin.

Ministan tace gaba daya kasafin shekarar ya kama tiriliyan N2.083, yayin da kudin kowacce gangar man fetur ake tammaninsa a dala 40, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square

FEC ta amince da N13.08trn na kasafin kudin 2021
FEC ta amince da N13.08trn na kasafin kudin 2021. Hoto daga @BasirAhmad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta

A wani labari na daban, kafin fara diban ma'aikata na musamman, gwamnatin tarayya ta mika wasiku ga a kalla bankuna shida domin bude asusu ga wadanda za a diba ayyukan.

Karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo, ya bayyana hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter, ya ce bankunan za su bude rassa na wucin-gadi a wasu kananan hukumomi da babu su.

Kamar yadda minsitan yace, bankunan sune: Zenith, UBA, Access, Fidelity, FCMB da Heritage, kuma gwamnati za ta sanar da bankunan kowacce karamar hukuma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel