Malaman Jami'a: Duk wanda baiyi rijista a IPPIS ba bai da rabo a kasafin kudin 2021 - Buhari

Malaman Jami'a: Duk wanda baiyi rijista a IPPIS ba bai da rabo a kasafin kudin 2021 - Buhari

- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2021 gaban majalisar dokokin tarayya

- Ya yi gargadin cewa da yiwuwan Najeriya ta sake komawa cikin matsin tattalin arziki

- Buhari ya ce ma'aikatan gwamnatin da basu cikin manhajar IPPIS basu da rabo a kasafin kudin

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ma'aikatan gwamnatin da aka yiwa rijista a manhajar biyan albashi ta IPPIS kadai zasu samu albashi a shekarar 2021.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi yayin gabatar da kasafin kudin N13.08 tiriliyan gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis a Abuja.

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU yanzu haka tana yajin aiki kuma ta lashi takobin cewa ba zata amince da manhajar IPPIS ba.

ASUU ta ce ta samar da nata manhajar wanda ya dace da ma'aikatan jami'o'in Najeriya.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce manhajar IPPIS ta haifar da matsaloli da kuma hanyoyin sata ga jami'an gwamnati.

A cewarsa, kokarin tilastawa lakcarori rijista a manhajar IPPIS ba tare da amincewarsu ba ya sa mambobinsu basu samu albashi ba na tsawon watanni uku zuwa takwas yanzu.

"Shin kun san wasu mambobinmu basu samu albashi ba tun watan Febrairu 2020. Manhajar IPPIS ba zata iya tafiyar da tsarin biyan albashi a jami'o'i ba." Ya ce

Amma shugaba Buhari ya ce wajibi ne dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya suyi rijista a manhajar ta IPPIS, saboda an yi hakan ne domin dakile rashawa da biyan ma'aikatan boge.

DUBA NAN: An yi zaman majalisar Sarki na farko karkashin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli (Hotuna)

Malaman Jami'a: Duk wanda baiyi rijista a IPPIS ba bai da rabo a kasafin kudin 2021 - Buhari
Credit: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A bangare guda, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce tattalin arzikin Najeriya zai iya sake komawa gidan jiya, watau cikin irin mawuyacin halin da ya taba shiga a baya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 a gaban mambobin majalisar tarayya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na gabatar da kasafin kudin 2021

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel