Gobara ta lashe gidan man fetur da shaguna 30 a kasuwa

Gobara ta lashe gidan man fetur da shaguna 30 a kasuwa

- Gobara ta tashi a wani gidan man fetur a Jihar Oyo da kuma kasuwa Katako a Jihar Plateau

- An shawarci mutane da su kara lura a lokacin sanyi don kauracewa annobar gobara

- Gwamnati tayi alkawarin kafa kwamitin da zai duba musabbabin gobarar tare da alkawarin tallafawa wanda suka yi asara

An ruwaito cewa wata babbar tankar man fetur ce ta kama da wuta dai dai lokacin da take juye mai a wani gidan mai da ke yankin Oluwole, Iseyin Saki a Jihar Oyo.

Kafin zuwan yan kwana kwana, ma'aikatan gidan man da makwabta suka yi bakin kokarin don shawo kan wutar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kwamandan yan kwana kwanan jihar Oyo, Mr Moshood Adewuyi, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce ba'a samu mutuwa ko rauni ba

Tankar dakon fetur ta kama da wuta a gidan mai, shaguna 30 sun kone ƙurmus
Tankar dakon fetur ta kama da wuta a gidan mai, shaguna 30 sun kone ƙurmus. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Bashir El-Rufai rike da Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka

"Gobarar ta tashi da misalin karfe 6:00 na yamma ranar Litinin dai dai lokacin da tankar mai ke juye mai. Mun gode Allah da ya kasance da nisa tsakanin famfon mai, kusan mita 400 daga inda lamarin ya faru. Rumfar gidan man da ofis da kuma harabar gidan man sun tabu," a cewarsa.

A wani labarin, kayayyakin miliyoyin Naira sun lalace bayan da wuta ta kama akalla shaguna 30 a kasuwar Shasha da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Shugaban yan kwana kwanan, Adewuyi, ya ce jami'an sa sun samu rahoto da misalin karfe 4:25 na asuba ranar Talata.

KU KARANTA: Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya, ta bayyana yadda za a iya samu

"Kusan shaguna 30 ne suka kone. Mun samu labarin cewa lamarin ya faru ne sakamakon gyara wutar lantarki da akayi ranar Talata. Shasha kasuwar kayan marmari da ganyayyaki ce, to kwandunan da aka tare ne suka ta'azzara wutar," a cewar sa.

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164