Rundunar Sojin Saman Najeriya ta karyata cewa Boko Haram ta harbo jirgi a Borno

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta karyata cewa Boko Haram ta harbo jirgi a Borno

- Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, ta ce ba gaskiya bane rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka wallafa na cewa Boko Haram sun harbo jirgi a yau Talata a Borno

- Kakakin Rudunar ta NAF, ya ce tabbas jirgin UN mai saukan ungulu ta tafi garin Banki a yau Talata amma ya koma Maiduguri kuma babu wanda ya mutu

- Hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad shima ya yi tsokaci kan batun idan ya ja hankulan kafafen watsa labarai su rika tantance rahoto kuma suyi gyara idan sun gano kuskure

Rundunar sojojin saman Najeriya, NAF, ta ƙaryata rahoton da kafafen watsa labarai suka wallafa na cewa Boko Haram to harbo jirgi mai saukan ungulu a Borno ta lashe mutum biyar.

Rahoton ya bazu sosai a shafukan intanet a yammacin yau cewa ƴan ta'adda sun harbo jirgi mai saukan ungulu a Banki, wani gari da ke Borno wadda ya yi sanadin rasuwar mutum biyar.

Karya ne, Boko Haram ba ta harbo jirgi mai saukan ungulu a Borno ba, in ji NAF
Karya ne, Boko Haram ba ta harbo jirgi mai saukan ungulu a Borno ba, in ji NAF. @KunleDaramola3
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan ƙwallon Najeriya ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a yayin buga wasa a Abeokuta

A martanin da ya yi ta shafin Twitter, Shugaban sashin watsa labarai da hulda da jama'a na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce rahoton ba gaskiya bane.

"Babu wani jirgi mai saukan ungulu a jihar Borno da aka harbo a yau. Wani jirgin UN mai saukan ungulu ya tafi Banki kuma tuni ya dawo Maiduguri."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ɗaliban ABU Zaria 17 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Kazalika, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari a fanin sabuwar kafar watsa labarai, Bashir Ahmad shima ya yi tsokaci kan labarin.

Ya bayyana cewa labarin ba gaskiya bane kana ya shawarci kafafen watsa labarai su rika tantance labari kafin su wallafa.

Ya ƙara da cewa idan kuma sunyi kuskure kamata ya yi su wallafa wani labarin su gyara kuskuren don al'umma su san gaskiyar lamarin ba suyi shiru su cire labarin ba daga shafinsu kawai.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel