Wabba: Karin farashin man fetur ya saba yarjejeniyar Gwamnati da NLC

Wabba: Karin farashin man fetur ya saba yarjejeniyar Gwamnati da NLC

- NLC ta nuna rashin amincewarta da karin farashin man fetur a Najeriya

- Ayuba Wabba ya yi tir da lamarin, ya yi kira ga gwamnati ta sake tunani

- Shugaban kungiyar kwadagon ya ce ana neman kai ‘yan Najeriya bango

Daily Trust ta ce kungiyar kwadago ta kasa, NLC ta fito ta yi magana a karon farko bayan gwamnatin tarayya ta kara farashin PMS, watau man fetur.

Kafin yanzu kungiyoyin kwadago na NLC da kuma TUC sun yi tsit game da karin kudin man da gwamnatin tarayya ta sake yi a ranar 13 ga watan Nuwamba.

Daga baya, shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba ya fitar da jawabi, ya na mai bayyana cewa kungiyar NLC sam ba ta goyon bayan wannan karin farashin.

KU KARANTA: Farashin man fetur ya sake tashi sama a Najeriya

Kwamred Wabba ya ce karin kudin man ya sake jefa mutanen kasar nan cikin matsi da wayyo Allah.

Ya ce: “Sabon karin farashin mai da aka yi, ya ci karo da yarjejeniyar da aka cin ma tsakanin gwamnati da ‘yan kwadago na tattaunawar karshe da mu ka yi.”

Jagoran ma’aikatan kasar ya ce gwamnatin tarayya ba ta yin abin da ya dace, ta bar ladanta. Wabba ya zargi gwamnatin da jawo wa kungiyar kwadago bakin-jini.

Wabba ya bayyana cewa su na sa ran ganin an gyara matatun mai kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyoyin kwadagon alkawari a zaman da su ka yi.

KU KARANTA: Gwamnati ta rage kudin takin zamani

Wabba: Karin farashin man fetur ya saba yarjejeniyar Gwamnati da NLC
Kwamred Ayuba Wabba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Akwai adadin abin da ‘yan kasa za su iya dauka idan aka cigaba da yin wannan karin kudin mai.” Inji Wabba.

A jawabin da ya fitar, shugaban kungiyar kwadagon ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba tsare-tsarenta da su ka yi sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi.

A jiya kun ji cewa karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya fadi dalilin tashin farashin mai. Hakan na zuwa ne bayan gwamnati ta kara kudin mai a kasar.

A cewarsa, tun bayan da Pfizer suka bayyana riga-kafin cutar COVID- 19 komai ya tashi a Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel