Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria

Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a rage farashin takin zamani domin wadatar da kasa da abinci

- A yanzu za a rinka sayar da takin akan N5000 mai makon N5500 da ake sayan sa a baya

- Wannan ragin da aka samu, na zuwa ne bayan da gwamnati ta kara farashin man fetur da lantarki a kasar

Domin tabbatar da samun wadataccen abinci ga yan Nigeria, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rage farashin taki da kaso mai yawa.

A cewar sanarwa daga Lauretta Onochie, hadimar shugaba Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, an zabtare farashin takin daga N5500 zuwa N5000.

KARANTA WANNAN: Kasar Saudiya ta amince a ci gaba da yin Umrah, ta gindaya sharudda

Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria
Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria
Asali: Depositphotos

Onochie ta bayyana cewa shugaban kasar ya yanke wannan shawara ne bayan shawarar da cibiyar wadatar da kasa da abinci (NFSC) ta ba shi.

Cibiyar NFSC na karkashin jagorancin Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu.

KARANTA WANNAN: Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu

Sanarwar Onochie na cewa: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a rage farashin taki daga N5500 zuwa N5000 akan kowanne buhu.

"An sanar da 'yan jaridu hakan ne jim kadan bayan ganarwar cibiyar NFSC karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi."

A wani labarin, Hukumar gudanarwar kasar Saudiya ta sanar da cewa, za ta bi matakai, wajen janye dokar dakatar da yin Umrah a Saudi Arabia da ta sanya sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Ministan aikin Hajj da Umrah, Mohammed Saleh Benten ya ce za su ci gaba da daukar lafiyar al'umma a kan komai, kuma ma'aikatarsa na duba matakai 3 na dawo da ibadar.

Shafin Haramain Sharifain a Twitter, ya sanar da cewa, matakin farko, za a amincewa mutane 6,000 yin ibada a kowacce rana, matakin zai fara daga ranar 4 ga watan Oktoba, 2020.

A mataki na biyu, za a amince mahajjata 15,000 su yi ibada a kowacce rana, da kuma masu yin Umrah 40,000 a kowacce rana, matakin zai fara daga ranar 18 ga watan Oktoba 2020.

A mataki na uku, za a dawo da aikin Umrah ba tare da doka ba, mutane na iya zuwa daga kowacce kasa, akalla Mahajjata 20,000 da masu Umrah 60,000 a kowacce rana.

Za a fara mataki na uku daga ranar 1 ga watan Nuwamba 2020, a cewar ma'aikatar cikin gida ta aikin Hajji da Umrah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel