Duk namijin da bashi da mata ba cikakke bane, bashi da farin ciki, Babban malami
- Henry Ibeanusi, babban mai wa'azi a jihar Enugu, ya ce namiji ba ya samun farinciki sai da aure
- A cewarsa, duk wadatar namiji, ba zai zama cikakken mutum ba, matsawar ba shi da mata
- Ibeanusi, ya janyo ayoyi daga cikin Bibul, wadanda suka nuna muhimmancin aure
A jihar Enugu, wani mai wa'azi, Ven. Henry Ibeanusi, a ranar Lahadi ya ce Ubangiji ya samar da aure don mutum ya samu cika da farinciki.
"Hakan yana nufin duk wani namiji ba ya samun cikar kamala da farinciki, matukar ba shi da aure," cewar Ibeanusi a wani wa'azi da yayi a cocin Anglican dake jihar Enugu.
Ibeanusi ya ce, Adam shine mutumin da yafi kowa wadata a duniya a lokacinsa, yana da dabbobi, ma'adanai da wuri mai yalwa, amma bai samu farin ciki ba sai da Ubangiji ya samar masa da mata.
Kamar yadda yace, bayan Ubangiji ya lura da rashin farinciki da rashin nutsuwarsa, a fasaha ta Ubangiji ya samar masa da mata.
"Mace tana da muhimmiyar rawa da take takawa a rayuwar namiji, wurin samar masa da farinciki, iyali da kuma gyara masa gida," a cewarsa.
Ibeanusi ya sanar da hakkokin miji, matarsa, yara da kuma masu aikin gida da suke zaune, kamar yadda Bibul ya sanar, a kan soyayya da tausayi tsakanin juna.
KU KARANTA: Yadda masu garkuwa da mutane suka dinga lalata da mu kafin su sake mu, 'Yan matan Katsina
KU KARANTA: Bidiyo da hotunan ragargazar da soji suka yi wa 'yan bindiga yayin da suke kwashe shanu a Kaduna
A wani labari na daban, wata jarumar fina-finan Nollywood, Olive Utalor ta yi ikirarin mallakar duk wani abu da zai karkato da hankalin namiji a aure, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Jaruma Utalor ta fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da ita, inda ta tabbatar da yadda ta adana budurcinta har sai daren aurensu na farko.
Ta kara da cewa, ta tabbatar da yadda mijinta zai yi alfahari da ita, ta yadda ta adana budurcinta har aure.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng