Shugabancin kasa a 2023: PDP na fuskantar babban kalubale a kudu maso gabas
- Jiga-jigan 'yan jam'iyyar PDP na yankin kudu maso gabas, sun ce ba za ta sabu ba, bindiga a ruwa, dole ne a daukesu da muhimmanci
- Sun ce sun gaji da irin rikon sakainar kashin da PDP take yi musu, wajibi ne a tsayar da dan takara daga yankinsu
- A cewarsu, ba za su rike matsayin mataimakin shugaban kasa ba, kuma duk wani dan yankinsu da ya amshi matsayin, makiyinsu ne
Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP na yankin kudu maso gabas sun yi ikirarin barin jam'iyyar matukar APC bata tsayar da 'dan takarar shugaban kasa daga yankinsu ba.
Shugabannin PDP sun lashi takobin ba za su bari dan bangarensu ya zauna a matsayin mataimakin shugaban kasa ba, kuma za su dauki duk wanda ya amshi matsayin mataimakin shugaban kasa a matsayin makiyin yankin.
Tsohon gwamna dake yankin ya sanar da Vanguard cewa tun 1998 kudu maso gabas take cikin wannan yanayin, tana biyayya ga PDP duk da abubuwan da suka faru da tsohon mataimakin shugaban kasa, Dr Alex Ekwueme a wani taro a Jos.
KU KARANTA: Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno
A cewarsa: "Idan jam'iyyar PDP ta ki tsayar da mai takarar shugabancin kasa a 2023 daga yankin kudu maso gabas, dole za mu bar jam'iyyar.
"Muna bayan dan uwanmu, gwamnan jihar Ebonyi Engr. David Umahi. Mun dade muna bin bayan PDP, ba zai yuwu su yi mana rikon sakainar kashi ba.
"Mun kuma rantse ba za mu amince da rike kujerar mataimakin shugaban kasa ba, sannan duk wani na mu da ya amshi kujerar, makiyinmu ne."
Dole ne a dinga yi musu adalci a jam'iyya, kuma a saka mana da alkhairi, Vanguard ta wallafa.
"Ga dukkan alamu, APC tana kokarin tsayar da dan takararta daga yankin kudu maso gabas, don haka bazamu yarda a daukemu a wawaye ba." suka ce.
KU KARANTA: Mata sun fi kasancewa cikin farin ciki ba idan basu tare da maza, Jaruma Inem
A wani labari na daban, Sanata Ali Ndume ya zargi tubabbun 'yan Boko haram bai wa 'yan ta'addan bayanai a kan sojoji, musamman bayan ganin harin da suka kai Damboa kwanan nan.
Ndume, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar tarayya ta sojoji, ya sanar da hakan lokacin gabatar da kasafin sojoji a gaban kwamitin, ranar 11 ga watan Nuwamba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng