Shugaba Manuel Merino ya yi murabus bayan zanga-zanga ta kaure a Peri

Shugaba Manuel Merino ya yi murabus bayan zanga-zanga ta kaure a Peri

- Manuel Merino ya sauka daga kan kujerar Shugaban kasa a Peru

- Merino ya karbi mulki ne bayan tsige Martin Vizcarra kwanan nan

- Duka-duka, kwanaki biyar ne Merino ya shafe a kan karagar mulki

A ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, 2020, shugaban kasar Peru, Mista Manuel Merino, ya yi murabus daga kan karagar mulki.

Jaridar Vanguard ta ce shugaba Manuel Merino ya bar kujerar mulki ne kwanaki biyar kacal da zamansa shugaban kasar Peru.

Murabus din da Merino ya yi ta sa jama’a sun fito su na farin ciki a titunan Peru. Hakan na zuwa ne bayan ya yi ta fama da zanga-zanga.

KU KARANTA: Hotunan gidaje da motocin Sadio Mane

“Ina so duka kasar nan su san cewa zan yi murabus.” Shugaba Merino ya shaida wa jama’a a lokacin da ya yi jawabi a gidan talabijin.

Shugaban kasar ya bayyana murabus din na sa ne bayan mutane akalla biyu daga cikin masu zanga-zanga sun mutu a hannun yan sanda.

Shugaba Merino ya tabbatar da ajiye mukaminsa ne jim kadan da ‘yan majalisa su ka huro masa wuta cewa ya yi murabus, ko su tunbuke shi.

A na sa ran majalisar kasar nahiyar Amurkan ta zabi sabon shugaban kasa nan ba da jima wa ba.

Shugaba Manuel Merino ya yi murabus bayan zanga-zanga ta kaure a Peri
Shugaba Manuel Merino Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Christian Obodo ya fada hannun masu garkuwa da mutane

Shugaban kasar da za a nada zai zama mutum na uku da ya rike ragamar Peru cikin kusan mako guda bayan tsige shugaba Martin Vizcarra.

Wasu daga cikin ministocin kasar da aka rantsar ranar Alhamis za su cigaba da rike mukamansu domin gudun barin kasar babu wasu shugabanni.

Dazu kun ji cewa tsohon Tauraron Super Eagles, Christian Obodo, ya sake shiga hannun Miyagu. Da ya ke akwai sauran kwana a gaba, ya samu 'yanci.

An taba yin garkuwa da Obodo a shekarun baya har sai da aka biya 'yan bindigan kudin fansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel