Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu

Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu

- Sadio Mane daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa ne wanda ya mallaki motocin hawa na alfarma

- Dan wasan kwallon kafan yana da matukar natsuwa a duk inda aka ganshi, kuma a kan samesa yana tuka motocin alfarma

- Mane yana da motocin da darajar kudinsu ya kai $665,000, wanda yayin daidai da kusan miliyan 256

Sadio Mane fitaccen dan wasan kwallon kafa ne da ke matukar son motocin alfarma.

Fitaccen dan wasan kwallon dan asalin kasar Senegal yana da gareji mai cike da motoci da suka kai darajar dala 665,000 wanda yake daya da miliyan 256.

Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Liverpool din ya mallaki mota kirar Marsandi G63 AMG mai darajar $200,000 wacce naira miliyan 78, Bentley Continental GT mai darajar $200,000 wacce take naira miliyan 78, Audi RS7 mai darajar $120,000 daidai da 46 miliyan da kuma Range Rover Evoque mai darajar $45,000 daidai da N17 miliyan.

KU KARANTA: Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya

Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu
Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu.
Asali: Getty Images

Amma kuma ana yawan ganinsa yana tuka motarsa kirar Range Rover a wurin horarwa kuma daga abinda kowanne dan kwallo ke samu, zai iya siyanta a kowanne minti 33.

Mane yana da kudin da suka kai $20 miliyan wanda yayi daidai da N7.7 biliyan a 2020. Hakan yasa ya zama daya daga cikin 'yan kwallo massu arziki a duniya.

KU KARANTA: Da duminsa: Akeredelu ya lallasa Jegede, ya yi nasara da tazarar kuri'u masu yawa

A wani labari na daban, manema labarai, wakilan jam'iyyu da kuma masu lura da zabe sun tarwatse inda suka dinga neman maboya sakamakon ruwan wutar da ake musaya tsakanin 'yan sanda da 'yan daba.

Lamarin ya faru ne a makarantar firamare ta St Peter da ke Akure a ranar Asabar. Ana amfani da makarantar firamaren wurin tattara sakamakon zaben karamar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar Ondo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel