Yadda budurwa dauka matashi mai talla a titi, ta sauya masa rayuwarsa gaba daya

Yadda budurwa dauka matashi mai talla a titi, ta sauya masa rayuwarsa gaba daya

- Nana Aba Anamoah ta canja raayuwar wani mai talla a bakin titi, mai suna Ebetoda, har ya zama ma'aikacin gidan talabijin

- Nana ta hadu da Ebetoda da abokinsa suna talla a bakin titi, inda tayi alkawarin za ta tallafi rayuwarsa

- Makonni 6 da haduwarsu, Nana ta tallafa wa raywarsa ta sama masa aiki a gidan Talabijin din Agoo

Nana Aba Anamoah, ta canja rayuwar wani mai talla a kan titi, inda ta taimaka masa har ya cika burinsa na rayuwa. Bayan haduwarsu da makonni kadan, saurayin mai suna Ebetoda ya samu cikar burinsa.

A ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba, 2020, Nana ta wallafa wani bidiyo, wanda ta hadu da wasu samari 2 a titi.

Bayan samarin sun ga Nana a mota, sun biyo ta suna yi mata bambadanci, har suna rokonta ko zasuyi hoto tare.

A cikin samarin 2 akwai Ebetoda, wanda ya bayyana yadda yake mutukar son zama ma'aikacin gidan talabijin, amma rashin kudi ya hana shi.

Yadda budurwa dauka matashi mai talla a titi, ta dauka nauyin karatunsa
Yadda budurwa dauka matashi mai talla a titi, ta dauka nauyin karatunsa. Hoto daga thenanaaba
Asali: Instagram

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan ragargazar da soji suka yi wa 'yan bindiga yayin da suke kwashe shanu a Kaduna

Bayan samarin sun ziyarci ofishinta, har ta siyo musu abinci, ta yi masa alkawarin taimakonsa don ya cika burinsa.

Nana Aba ta dage wurin sama masa aiki, inda ta samar da sabon shiri musamman saboda shi a gidan talabijin din Agoo

Har Nana Aba ta wallafa samfotin shirin da saurayin zai fara gabatarwa a shafinta na Instagram.

KU KARANTA: Na mallaki duk abinda namiji zai bukata, na killace masa budurcina - Jaruma Fim Utalor

A wani labari na daban, hukumar 'yan sandan jihar Bauchi, sun kama wani saurayi mai shekaru 18, bisa zargin yanka wani saurayi a kan budurwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa hakan.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Ahmed Wakil, ya sanar da hakan a wata takarda da ya saki a kan lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel