Da duminsa: Sabbin mutum 152 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya
- Sabbin alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa na ranar Lahadi ya bayyana cewa sabbin mutum 152 sun sake harbuwa
- Kamar yadda alkalumman suka bayyana, an samu mutum 136 a jihar Legas, 4 a jihar Kano, 3 a jihar Neja sai 2 a jihar Ekiti
- Jimillar mutanen da suka taba kamuwa da muguwar cutar a Najeriya suna kai mutum 65148 a fadin kasar nan
Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta bayyana na ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2020, sabbin mutum 152 sun sake kamuwa da cutar korona a fadin Najeriya.
Lagos-136
Kano-4
Niger-3
Ekiti-2
Kaduna-2
Ogun-2
Taraba-2
FCT-1
KU KARANTA: Saurayi ya halaka abokin takararsa wurin neman soyayyar budurwa a Bauchi
Jimillar mutanen da suka kamu da cutar a fadin Najeriya sun kai 65148, wadanda aka sallama daga asibiti bayan warkewarsu sun kai 61073, yayin da mutum 1163 suka riga mu gidan gaskiya sakamkon muguwar cutar.
KU KARANTA: Na mallaki duk abinda namiji zai bukata, na killace masa budurcina - Jaruma Fim Utalor
A wani labari na daban, a jihar Enugu, wani mai wa'azi, Ven. Henry Ibeanusi, a ranar Lahadi ya ce Ubangiji ya samar da aure don mutum ya samu cika da farinciki.
"Hakan yana nufin duk wani namiji ba ya samun cikar kamala da farinciki, matukar ba shi da aure," cewar Ibeanusi a wani wa'azi da yayi a cocin Anglican dake jihar Enugu.
Ibeanusi ya ce, Adam shine mutumin da yafi kowa wadata a duniya a lokacinsa, yana da dabbobi, ma'adanai da wuri mai yalwa, amma bai samu farin ciki ba sai da Ubangiji ya samar masa da mata.
Kamar yadda yace, bayan Ubangiji ya lura da rashin farinciki da rashin nutsuwarsa, a fasaha ta Ubangiji ya samar masa da mata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng