An kama dattijan ma'aurata bisa zargin datse hannaye da kan gawar matashi

An kama dattijan ma'aurata bisa zargin datse hannaye da kan gawar matashi

- An gurfanar da wasu dattijan ma'aurata a gaban kotu bisa zarginsu da datse kai da hannun gawar wani matashi

- Dattijan ma'auratan ma su shekaru sittin a duniya sun musanta tuhumar da ake yi musu a gaban kotu

- An fara gurfanar da ma su laifin a gaban kotun majistare da ke Osogbo, jihar Osun, tun cikin watan Maris

Rundunar ƴansandan jihar Osun ta gurfanar da ma'aurata masu shekaru sittin; Ashifat Okunade da Ashifat Mariam, a gaban wata kotun majistire dake Osogbo bisa zargin yanke kai da hannun gawa.

Mai gabatar da ƙarar ya gurfanar da ma'auratan a watan Maris 2020, amma sai daga baya ya canja tuhumar da wani sabon zargin daban wanda ya karantawa waɗanda ake zargin.

Ɗansanda mai gabatar da ƙara, John Idoko, ya shaidawa kotun cewa; "waɗanda ake zargin da wasu mutane a ranar 21 ga watan Maris, 2020, da misalin ƙarfe ɗaya na rana, a unguwar Dagbolu da ke yankin Ifon sun aikata wani ƙaramin laifi ko ince shiga hurumin gawar wani bawan Allah, Rasheed Tiamiyu, inda suka datse kai da hannuwan mamacin.

KARANTA: A karshe: Donald Trump ya saduda, ya karbi faduwa tare da yin sambatu

"Laifin ya saɓawa doka kuma akwai hukunci a ƙarƙashin sashe na 242 na kundin manyan laifuka, saɗara ta 34, Littafi na biyu na jihar Osun da aka kirkira a shekarar 2002".

An kama dattijan ma'aurata bisa zargin datse hannaye da kan gawar matashi
An kama dattijan ma'aurata bisa zargin datse hannaye da kan gawar matashi @Thecable
Asali: Twitter

Sai dai, ma'auratan sun yi kememe tare da bayyana cewa basu aikata laifin shiga hurumin mamacin ba.

Lauya mai kare ma'auratan, Yemisi Akintajuwa, ya roƙi babban alƙalin kotun da ya bada belin. masu laifin.

KARANTA: Saurayi ya bankawa kansa da budurwarsa wuta bayan ya malale dakinsu da fetur

Babban alkalin kotun, Dakta Olusegun Ayilara, ya ce waɗanda ake zargin za su cigaba da cin moriyar belin da aka bayar dasu tun a tuhumar baya kana ya ɗage cigaba da sauraron shari'ar zuwa 8 ga watan Junairun shekarar 2021.

Legit.ng Hausa ta taba wallafa rahoton cewa 'yan sanda a jihar Neja sun kama wasu mutane hudu da kan mutum a kauyen Sabon Pegi da ke karamar hukumar Mashegu.

Binciken 'yan sanda ya gano cewa wani mutum mai suna Abdullahi Dogo shine jagoran sauran mutanen da aka kamasu tare.

Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Dogo ya bayyana cewa ma su sayen sassan jikin mutum ne su ka dauke shi kwangilar tono mu su sabuwar gawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng