'Yan jihar Kaduna za su fara biyan harajin 1,000 a kowacce shekara, KADIRS
- Hukumar amsar haraji ta jihar Kaduna, KADRIS, za ta wajabta wa duk wanda ya mallaki hankalin kansa biyan harajin N1000 duk shekara
- A cewar shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar, daga ranar Laraba, za a fara amsar harajin da za a yi amfani dashi a 2021
- Amsar harajin zai taimaka wurin bubbugo da tattalin arzikin jihar don samu ayi wa jihar gyare-gyaran tituna da ma'aikatu
KADRIS ta ce za ta fara amsar N1000 don cigaban jihar na 2021 daga hannun duk wanda ya mallaki hankalin kansa, kuma mazaunin jihar Kaduna.
Hakan zai cigaba ne duk shekara, Daily Nigerian ta ruwaito.
Shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna, inda yace daga shekarar 2021, duk wani mai hankalin kansa da yake zaune a jihar wajibi ne ya biya wannan harajin.
Ya ce hakan yayi daidai da sashi na 9 (2) na dokar amsar harajin jihar Kaduna na 2020.
Ya kara da cewa, doka ta wajabta wa duk wani mai hankalin kansa da yake zama a jihar ya dinga biyan N1000 a matsayin ta sa gudunmawar don gyaran ma'aikatun jihar da kuma kara wa jihar kudin shiga don yin ayyuka yadda suka dace.
KU KARANTA: 'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma
"Za a samu wannan nasarar ne idan ana biyan haraji, wanda zai koma ga tattalin arzikin jihar don kowa ya kurbi romon demokradiyya.
"Kamar yadda aka kira harajin, kudin samar da cigaba, tabbas hakan zai kawo cigaban jihar.
"Dukkan mu shaidu ne a kan yadda tattalin arzikin jihar nan yake lalacewa kullum.
"Wannan zai bayar da damar gyaran tituna, asibitoci, gyara ma'aikatu, samar da kayan aiki a asibitoci da makarantu da gyara duk wata baraka," a cewarsa.
KU KARANTA: Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a
A wani labari na daban, tubabbun 'yan Boko Haram ne sukayi sanadin mutuwar kanal din sojojin kasa, Kanal D.C Bako, a cewar sanatan jihar Borno, Ali Ndume.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng